Bam ya fashe kusa da sashen mata a jami'ar Maiduguri

A watan Janairu 2017 an kai hari a wani masallaci dake cikin jami'ar Maiduguri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Janairu 2017 an kai hari a wani masallaci da ke cikin jami'ar Maiduguri

A Najeriya, wasu mazauna birnin Maiduguri na jihar Borno sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa a jami'ar Maiduguri.

Lamarin dai ya faru ne tsakanin daren ranar alhamis da kuma safiyar ranar Juma'a.

Babban jami'in hukumar bayar da agajin gaggawaNEMA, mai kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Muhammad Kanar ya tabbatar wa da BBC fashewar abubuwan.

'Yan ƙunar baƙin wake sun tarwatsa kansu a Jami'ar Maiduguri

Maiduguri: An daure 'barayin' shinkafar 'yan gudun hijira

Bidiyon masallacin da BH suka rusa a jami'ar Maiduguri

Shin wanene farfesan da BH ta kashe a Maiduguri?

Rahotanni sun ce wasu 'yan kunar bakin wake maza ne guda uku suka nufi sashen dakunan mata na jami'ar don tayar da bam din, amma sai ya tashi da su kafin su karasa.

Dukkan 'yan kunar bakin waken sun mutu. Daya daga cikin su na dauke da bindiga kirar AK 47.

A kalla bama-bamai biyu ne suka fashe yayin kai hare-haren.

Wani Malami a jami'ar ya tabbatar da cewa bam din ya fashe ne a kusa da sashen dakunan kwanan dalibai mata na BOT.

Ya kara da cewa wani bam din kuma ya sake tashi a kusa da bangaren kiwon lafiyar dabbobi na jami'ar.

Wani ma'aikacin bayar da agaji da aka yi aikin ceto da shi ya ce, "Ba wanda ya mutu a harin baya ga 'yan kunar bakin waken, amma wasu jami'an tsaron jami'ar hudu sun samu raunuka kuma tuni an ba su taimakon da ya dace.

Tuni dai hukumar NEMA ta kwashe gawarwakin 'yan kunar bakin waken da suka mutun.

A baya-bayan nan ana samun karuwar kai hare-hare birnin Maiduguri da kuma jami'ar birnin. Ko a ranar 13 ga watan Mayun nan ma wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari jami'ar.

Labarai masu alaka