Japan: Sarki Akihito zai yi murabus

Sarki Akihito ya shafe shekaru 25 yana mulki a Japan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Akihito ya shafe shekaru 25 yana mulki a Japan

Gwamnatin kasar Japan ta amince da wani shiri na barin Sarkin Sarakuna Akihito yin murabus, wanda shi ne irinsa na farko da aka taba yi cikin karni biyu.

Majalisar zartarwar kasar ta amince da wani daftarin doka da za'a aikewa 'yan Majalisun dokokin kasar don neman amincewar su.

A bara ne dai Sarkin, mai shekaru 83 ya bayyana aniyarsa ta sauka daga karagar mulki saboda rashin lafiya, bayan ya shafe fiye da shekaru 25 kan gadon sarauta.

Matukar 'yan Majalisun dokoki sun amince da dokar, to dan sa, Yarima Naruhito ne zai gaje shi.

Labarai masu alaka