Nigeria: Iyayen 'yan Chibok na hanyar zuwa ganin 'ya'yansu

Shugaba Buhari ya gana da 'yan matan kafin ya wuce Ingila
Image caption Shugaba Buhari ya gana da 'yan matan kafin ya wuce Ingila

A Najeriya, iyayen 'yan matan Chibok 82 da aka ceto kwanan nan, gami da 21 na baya, na bisa hanyarsu ta zuwa Abuja daga garin Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, domin yin ido hudu da 'ya'yan nasu.

Makwanni biyu da suka gabata ne Shugaban iyayen na Chibok, Yakubu Nkeki, ya je Abuja domin ganin 'yan mata 82 da aka ceto ta hanyar musayar fursunonin Boko Haram, kuma ya koma wa iyayen nasu da hotunansu domin su tabbar da 'ya'yan nasu.

Iyayen na fatan zasu gana da 'ya'yan, a karo na farko bayan da kungiyar Boko Haram ta sace su a makarantarsu, shekara uku da suka gabata.

Wani daga cikin mahaifan ya ce suna fatan isowa cikin lafiya don su samu ganin 'ya'yansu.

Ya kuma ce baya ga iyayen yaran akwai wasu manyan garin don su yi musu rakiya daga Chibok zuwa Abujan.

Tawagar iyayen dai sun kai mutum 200.

Labarai masu alaka