Mece ce makomar 'yan matan Chibok?

'Yan matan Chibok sun ci kwalliya.
Image caption Ba a bar 'yan matan Chibok sun yi magana da manema labarai ba

A watan Afrilun shekarar 2014 ne, 'yan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da 'yan mata 276 da suke makarantar Chibok a arewa maso gabashin Najeriya.

A wannan watan da muke ciki ne aka sako da dama daga cikinsu.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, yaushe ne za a sako sauran?

Tun daga shekarar 2009 da 'yan Boko Haram suka fara kai hare-haren ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya.

Ana tsaka da alhinin garkuwa da 'yan matan ne, 57 daga cikinsu suka tsallake rijiya da baya, inda aka nausa da ragowar can cikin dajin Sambisa.

Tun bayan sama da shekara uku da sace yaran suke matsawa daga dajin zuwa birni, ko koguna, inda suke gararamba a tsakanin arewa maso gabashin Najeriya.

Image caption Sojojin Najeriya sun ce sai sun murkushe Boko Haram

Matsin lambar da aka yi wa 'yan Boko Haram din da wadanda suka kama, ta sa rayuwa ta yi musu kunci, wasu lokutan ma yaran ba sa iya samun abinci sau daya a rana.

A cikin dare ne yaran 82 suka tafi wurin da aka kulla yarjejeniyar karbar su suna jira a gefen dajin kusa da iyakar Kamaru.

Ba su san abin da ke shirin faruwa a kansu ba, sai dai sun yi layi a cikin duhu, sanye da dogayen hijabai, da wasu maza bakwai suna gadinsu. Wani ne yake kiran sunayensu daga cikin jerin sunayen da aka fitar, inda suke tafiya wurin mutumin da ya jagoranci karbar su don ya tafi da su.

Daga baya mutumin da ya jagoranci karbar su ya ce, an tambayi kowacce daga cikinsu da karfi, cewa, "Tsawon lokacin da kuka zauna tare da mu, akwai wanda ya yi muku fyade ko ya yi muku makamancin haka?" Dukkanninsu sun amsa da a'a.

Daga nan suka ce musu yau dai kun samu 'yanci. Sai suka ruga a guje suka fara shiga mota suna tafi suna wakoki na nuna farin ciki.

Ba tare da wani bata lokaci ba aka dauki hanyar fitowa daga dajin cikin ayarin motoci.

'Yan matan 82 da aka sako sun gana da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Image caption Shugaba Buhari ya ce 'yan Chibok sai sun cika burinsu na yin karatu
Image caption An yi bikin nuna murna kan sakin 'yan matan

Yawancin 'yan matan Kirista ne a lokacin da aka sace su, amma yanzu yawancinsu sun shiga addinin Musulunci, kuma wwatakila an tilasta musu ne ko kuma suna ganin za su fi samun jin dadin zama da su idan suka musulunta.

Yakubu Nkeki mahaifin daya daga cikin 'yan matan ne kuma ya ce, "Lokacin da na fara ganinta sai ta yi tsalle ta rungume ni, ni ma na rungume ta. Na rike ta muka fara rawa muna juyawa a wurin.Ta fara dariya, sannan sai ta fashe da kuka. Da na tambaye ta dalili sai ta ce, saboda ba ta taba tunanin za ta kara gani na ba."

An saki biyar daga cikin 'yan mata bakwai da aka kama daga danginsa.

'Yau rana ta musamman ce ga 'yan matan Chibok'

Ba wannan ne karo na farko da aka sako 'yan matan Chibok ba. Ko a watan Oktoban shekarar da ta gabata, an kubuto da 21 bayan wata doguwar tattaunawa.

Sai dai sun rame kuma ba su da isasshiyar lafiya, amma dai da ransu.

Image caption Michelle Obama na cikin wadanda suka jawo hankalin duniya kan sace matan

A watan Oktoban shekarar da ta gabata, ministar harkokin mata Aisha al-Hassan ta jagoranci sakin 'yan matan 21 a wata ganawa da suka yi da shugaban kasar Najeriya.

Idan a mota za a zo Abuja daga Chibok zai dauki tsawon kawan biyu. Domin nisan tafiyar ya kai kilomita 900, kuma yawancin iyayen yaran ba za su iya biyan kudin motar zuwan ba.

Suna karkashin kulawar jami'an tsaro, tare da kulawar ministar harkokin matan Najeriya Aisha Jumai al-Hassan.


A lokacin da suke kan layi, an tambaye su su yi bayani a kan irin rayuwar da suke so su yi a cibiyar kulawa ta gwamnati.

'Yan matan sun bayyana darrussan da suka fi so wadanda suka hada da biology, chemistry da physics da kuma wasanni, domin suna son wasa.

Image caption Amina Ali (daga hagu) da jaririnta ya yin ganawa da shugaba Buhari.
Image caption 'Yar Chibok din da ta zabi zama da Boko Haram

Ana ta yamadidi da wani bidiyo da yake nuna yarinyar da take ikirarin cewa ta fi kaunar zama da 'yan Boko Haram fiye da 'yan uwanta.

A cikin bidiyon an nuna yarinyar tana dauke da bindiga kirar AK-47 tare da yin bayanin dalilinta na son zama a can.

Yarinyar ta ce, "Iyayena kafirai ne, muna son su Musulunta mu hadu wajen gudanar da ayyukan addini."

Mahaifiyar yarinyar na cikin kungiyar da ke fafautukar ganin an ceto 'yan matan mai suna #BringBackOurGirls.

Kadan ne suka san hakikanin abin da ya faru da su a hannun Boko Haram, saboda ba a ba su damar yin magana da manema labarai ba.

Hikimar gwamnati ta yin hakan ita ce don a yi kokari a ga sun manta da abubuwan da suka gamu da su maimakon su rike su a ransu.


'Jadawalin sace 'yan matan Chibok'

'Yan mata 276 aka sace a ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

Bayan kwanaki kadan 57 suka tsallake rijiya da baya.

18 ga watan Mayun shekarar 2016 daya ta tsere aka kuma same ta.

13 ga watan Oktoban 2016 aka saki 21.

17 ga watan Nuwambar 2016 daya da tsare aka sameta a hannun sojoji.

Biyar ga watan Janairun 2017 daya ta tsare kuma an sameta.

Shida ga watan Mayun 2017 aka sako 82.

Har yanzu akwai ragowar 113.