Kun san abin da Trump ya je yi Saudiyya?

Donald Trump Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Trump zai kai ziyarar rangadi zuwa saudiyya

Shugaban Amurka Donald Trump zai kai ziyarar ran gadi ta farko bayan hawansa karagar mulki zuwa kasahen Saudiyya, da Isra'ila da kuma fadar Vatican. Wato kasashen cibiyar manyan addinan Musuluci, da Kiristanci, da kuma Yahudanci.

Kasar Saudiyya dai ta yi mamaki yadda Mista Trump ya zabe ta a matsayin kasa ta farko a ziyarar rangadinsa, tun bayan hawansa karagar mulki.

Kasar wacce ita ce tushen Musulunci, kuma kasa da mahajjata a fadin duniya ke taruwa domin gudanar da aikin hajji, na karbar bakuncin mutumin da aka zarga da kin jinin Musulunci, saboda yunkurinsa wanda bai samu nasara ba, na haramta wa wasu kasashen Musulmai shida shiga Amurka.

A lokacin yakin neman zabensa na watan Febrairun 2016, ya ce jami'an saudiyya na da hannu a hare-haren 11, ga watan Satumbar 2001.

A matsayinsa na shugaban kasa, Mista Trump na ganin cewa abin da kawai zai nesanta shi da manufofin kasashen waje na shugaba Obama shi ne, ya watsar da Iran, ya kuma kulla alaka da Saudiyya.

Bayan da ya karbi mulki a watan Janairu, ya tura Daraktan leken asirin kasar, Mike Pompeo, zuwa Saudiyya da Bahrain, in da ya samu kyakkyawar tarba.

Hakkin mallakar hoto FRANK GARDNER
Image caption Ziyarar za ta kara karfafa danganta tsakanin kasashen biyu

Abin da ya kara kulla sabuwar dangantaka tsakanin kasahen Amurka da Saudiyya, shi ne ziyarar da Yariman kasar kuma Ministan Tsaro, yarima Muhammad Bin Salman ya kai fadar White House a watan maris.

To me ake tunanin cewa za a tattauna idan tawagar shugaban Amurka ta sauka a birnin Riyadh?

Da'addanci da tsaro

Yadda za a magance kalubalen ta'addanci, musamman kungiyar IS (ko "daesh" kamar yadda Larabawa ke kiranta da shi), shi ne zai mamaye tattaunawar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Amurka na taimakawa Saudiyya

Hukumar leken asirin Amurka, tare da hukumomin leken asirin kasashen yamma da kuma rundunar tsaro ta musamman, na taimaka wa hukumomin Saudiyya wajen kawar da ta'addanci tun lokacin da kungiyar al'Qaeda ta fara rikicinta a 2003, da kuma tun harin Makka da aka kai a shekarar 1979.

Matsalar kasar Iran

Shugabannin Saudiyya na kallon kasar Iran da kungiyar da take mara wa baya a matsayin babbar barazana ga yankin gabas ta tsakiya, zargin da Iran din ta sha musantawa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saudiyya na yi wa Iran kallon babbar barazana a Gabas Ta Tsakiya

Haka suma kasashe makwabta irin su Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa na yi wa Iran kallon babbar barazana. Haka su ma manyan jami'an gwamnatin Amurka kamar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar H R McMaster, da kuma sakataren tsaro James Mattis

Harkokin kasuwanci

Wasu rahotonni da na cewa yana fatan a ziyarar tasa zuwa kasar Saudiyya ya jawo hankalin kasar ta zuba jari a kamfanonin Amurka har na kimanin dala biliyan 40.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana sa ran bunkasa harkokin kasuwanci

Labarai masu alaka