Hassan Rouhani ya lashe zaɓen Iran karo na biyu

Mr Rouhani (na tsakiya) ya kada kuri'arsa a Tehran, babban birnin kasar. Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Mr Rouhani (na tsakiya) ya kada kuri'arsa a Tehran, babban birnin kasar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya lashe zaben kasar karo na biyu, in ji wata sanarwa da gidan talabijin na kasar ya bayar.

Gidan talabijin din na gwamnati ya kara da cewa shugaban kasar ya samu fiye da rabin kuri'u 40m da aka kirga.

Mr Rouhani, mutumin da ke da matsakaicin ra'ayi wanda ya amince da yarjejeniyar da kasarsa ta kulla da kasahen yammacin duniya domin ta rage kera makamashin nukiliya, ba sai ya fuskanci zuwa zabe zagaye na biyu ba.

Babban mai hamayya da shi ya yi korafin cewa an tafka magudi a zaben.

Ebrahim Raisi, mai tsattsauran ra'ayi, ya zargi magoya bayan Mr Rouhani da yin yakin neman zabe a wuraren kada kudi'a, sabanin dokokin zaben kasar.

Sakamakon zaben yankunan karkara - wanda ake ganin sun goyo bayan Mr Rouhani - bai fito ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutum 56m ne suka cancanci kada kuri'a

Gidan talabijin din kasar ya taya Mr Rouhani murna kan nasarar da ya yi.

Sakamakon zaben da aka kidaya ya nuna cewa ya samu kashi 58.6, yayin da shi kuma Mr Raisi ya samu kashi 39.8.

An tsawaita lokacin kada kuri'a da sa'o'i biyar ranar Juma'a, har tskar dare, sakamakon fitowar da mutane suka yi da yawa, inda aka yi kiyasi sun kai kashi 70 cikin 100.

Labarai masu alaka