Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya sake tayar da bam a Jami'ar Maiduguri

Jami'ar Maiduguri
Image caption An yi kira a katange dukkan Jami'ar Maiduguri

Wani dan ƙunar-baƙin-wake ya sake tarwatsa bam din da ke jikinsa a Jami'ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, kwana guda bayan wasu 'yan ƙunar-baƙin-waken sun kai hari.

Wani ganau na shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe a kusa da ginin da ake kira Enterprenuer building, cikin wani rami da sojoji suka tona.

Ya kara da cewa dan ƙunar-baƙin-wake ya buya ne a ramin da zummar yin ba-saja amma kawai sai bam din ya tashi da shi a lokacin yana cikin ramin.

Ganau din, wanda kuma Malamin Jami'ar ne ya kara da cewa wurin da lamarin ya faru yana can gefen Jami'ar kuma babu wani cikakken tsaro a wurin.

"Lamarin ya faru ne a kusa da Gate Five kuma wurin babu wata katanga da za ta hana wadannan mutanen haurowa cikin Jami'a. Ya kamata a gina babbar katangar da za ta kewaye wannan Jami'a idan ba haka ba 'yan Boko Haram za su ci gaba da haurowa suna yin barna", in ji shi.

A ranar Alhamis da tsakar dare zuwa wayewar garin Juma'a ma 'yan ƙunar-baƙin-wake uku sun tarwatsa kansu a Jami'ar ta Maiduguri.

Hakan ya faru ne bayan wasu 'yan ƙunar-baƙin-wake sun tayar da bama-baman da ke jikinsu mako biyu da suka wuce a cikin Jami'ar.

Labarai masu alaka