Korafin da 'yan kasuwar shanu ke yi a Maiduguri
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Korafin da 'yan kasuwar shanu ke yi a Maiduguri

Ita ce kasuwar shanu mafi girma a yankin Afirka ta Yamma
Image caption Ita ce kasuwar shanu mafi girma a yankin Afirka ta Yamma

Masu sana'a a kasuwar shanu ta Maiduguri da ke jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun koka kan rufe kasuwar da hukumomi suka yi wata biyar da suka wuce.

Kasuwar shanun ta Maiduguri - wacce aka bayyana mafi girma a yankin Afirka ta Yamma - ta shafe shekaru da dama ana harkar cinikayyar shanu da sauran dabbobi a ciki da wajen kasar.

Hukumomin dai sun ce sun dau matakin rufe kasuwar ne sakamakon bayanan sirrin da suka samu cewa mayakan Boko Haram na amfani da wasu dillalai a wannan kasuwa wajen samun kudin shiga.

Image caption Hukumomi sun ce an rufe ta ne saboda matsalar tsaro
Image caption 'Yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati ta sake bude kasuwar

Lokacin wata ziyara da wani ayarin BBC ya kai jihar Borno, Bilkisu Babangida ta ziyarci kasuwar shanun ta Maiduguri, ga kuma rahoto na musamman da ta hada mana.