Niger: An ceto bakin haure 30 a Sahara

Da dama dake kokarin ketarawa zuwa nahiyar Turai na mutuwa a cikin Sahara Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da dama dake kokarin ketarawa zuwa nahiyar Turai na mutuwa a cikin Sahara

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun ceto bakin haure sama da mutum 30 a cikin Sahara dake kokarin ketarawa zuwa nahiyar Turai.

Rahotanni sun ce sojojin Nijar ne suka ceto mutanen bayan da direban motar su ya barsu cikin Sahara lokacin da ce su jira shi ya je nemo ruwa amma ya bar su cikin tsakiyar Sahara.

Galibin mutanen da suka hada da mata sun fito ne daga wasu kasashen Afrika ta Yamma.

A halin yanzu hukumomin Nijar na shirye shiryen tesa keyar mutanen zuwa kasashen su na asali.

Wasu masana a Jamhuriyar Nijar sun ce duk da kokarin da hukumomin kasar ke cewa suna yi don magance kwararar bakin haure masu bi ta hanyar Agadas da zummar shiga kasashen Turai, har yanzu da sauran rina a kaba.