'A hukunta masu ta da zaune-tsaye a kudancin Kaduna'

Gwmnan Kaduna Nasiru El-Rufa'i
Image caption Gwamnatin jihar Kaduna ta lashi takobin magance rikice-rikicen addini da na kabilanci a jihar

Wasu 'yan asalin jihar Kaduna a Nijeriya sun yi kira ga hukumomi su dauki matakan ladabtar da duk wadanda aka samu da laifin ta da rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci a kudancin jihar.

Yayin wani taro da suka yi ranar Asabar, Musulmin kudancin Kaduna sun yi tsokaci kan rikice-rikicen da suka faru a yankin, musammam ma na lokacin zaben shekara ta 2011.

Mahalarta taron sun koka game da rashin hukunta masu aikata ta'asa a yankin duk da kwamitoci da dama waɗanda ke gabatar da rahotanni don gudanar da bincike.

Farfesa Abdullahi Musa Ashafa ya shaida wa BBC cewa mutane da dama sun mutu a yankin kudancin Kaduna lokacin rikicin bayan zabe a shekara ta 2011.

''Ya kamata a manta da bambance-bambancen addinai da kabilanci don samun dawwamammen zaman lafiya.''

Shi ma Alhaji Sanusi Dan Iyan Jema'a ya ce maslaha a yankin kudancin Kaduna za ta wanzu ne muddin mazauna yankin suka fahimci tarihi da kuma yadda dokar kasa take a zahirance;

"Tsarin mulki ya bai wa duk dan kasa damar ya zauna a duk inda yake so don haka bai kamata wasu su dauki doka a hannunsu su hallaka mutane ba."

Dan Iyan Jema'a ya kuma ce bukatarsu ita ce wadanda suka tafka asara a biya su diyya, a yi musu adalci, a gyara musu matsugunansu da wuraren ibadarsu;

"A tanadi matakan tsaro ta yadda duk dan kasa zai zauna a duk inda yake a Najeriya, ba tare da samun duk wata kafa ko damar da za a kashe ko cutar da shi ba."

Tsawon shekaru, kudancin Kaduna na daga cikin yankuna mafi fama da rikice-rikicen addini da ƙabilanci a Nijeriya, abin da kan haifar da mummunar asarar rayuka da dukiya.

Hukumomin jihar dai sun yi alƙawarin ɗaukar matakai game da waɗannan matsaloli, don samun wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Labarai masu alaka