Amurka ta yi tir da hare-hare kan Masallatai a Sri Lanka

Sri Lanka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani Masallaci a Sri Lanka

Amurka ta yi kira ga hukumomi a Sri Lanka da su dauki matakan gaggawa, bayan hare-haren da aka yi ta kai wa akan masallatai a fadin kasar.

A wani sako ta shafinsa na twitter, jakadan Amurka a Sri Lanka, Athul Keshap, ya yi kiran ganin an hukunta wadanda ke da alhakin hare haren ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce duk wani hari a kan wuraren ibada, abin Allah wadai ne.

A hari na baya bayan nan da aka kai yau Lahadi, wasu mutane sun jefa bama-baman fetur kan wani masallaci a arewa maso yammacin garin Kurunegala.

A daren jiya Asabar kuma, an kai hari kan shagon wani dan kasuwa musulmi a kudancin kasar.