Ta'addanci: Trump ya hori kasashen Musulmi

Saudi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Trump da sauran shugabannin kasashen Larabawa da na Musulmai a wajen taro a Saudiya

A wani muhimmin jawabi da ya gabatar wa shugabannin Larabawa da kasashen Musulmai, shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira gare su da su zama gaba-gaba wajen yaki da ta'addanci a kasashensu.

Da yake gabatar da jawabin a wajen taron kasashen a Saudiya, Mista Trump ya ce yaki da ta'addanci, yaki ne tsakanin abu mai kyau da mara kyau, ba wai tsakanin addinai ko ci gaban zamani ba.

Ya ce ya kamata kasashen Gabasa ta Tsakiya, su zaban ma kansu irin makomar da suke fatan su samu.

Mista Trump ya kuma soki Iran, wacce ya zarga da ruruta wutar rikice rikice da ayyukan ta'addanci a yankin, da kuma goyon bayan munanan laifukan da gwamnatin Assad ke aikatawa a Syria.