Zanga-zanga: An kona wani mutum a Venezuela

Wani dan sandan kwantar da tarzoma rike da garkuwa mai hoton Our Lady of Guadalupe lokacin da jami'an tsaro suka kara da masu goyon bayan 'yan adawa a wajen wata zanga-zangar kyama da shugaba Nicolas Maduro a Caracas, Venezuela ranar 20 ga Mayu 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe mutane masu dama kuma daruruwan mutane sun jikkata lokacin wannan zanga-zangar kin jinin gwamnati

Wani dan sandan kwantar da tarzoma rike da garkuwa mai hoton "Our Lady of Guadalupe" lokacin da jami'an tsaro suka kara da masu goyon bayan 'yan adawa a wajen wata zanga-zangar nuna kyama ga shugaba Nicolas Maduro a birnin Caracas, Venezuela ranar 20 ga Mayu 2017.

Gargadi: Akwai hotuna masu iya tayar da hankali a cikin wannan rahoton.

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya tuhumi 'yan adawa da kona wani mai goyon bayan gwamnatinsa a birnin Caracas a rana ta 50 da fara zanga-zangar da ta mamaye kasar.

Mutumin mai suna Orlando José Figuera ya sami kunar wuta a kashi 80 cikin dari na jikinsa. Jami'ai sun ce kuma an daba masa wuka a yayin zanga-zangar ta ranar Asabar.

Wasu da suka shaida abin da ya faru sun ce masu zanga-zangar sun tuhume shi da yin sata ne.

A wannan yinin ne kuma aka sami rahoton harbe wani dan adawa har lahira, batun da ya kai yawan wadanda suka rasa rayukansu zuwa 48.

Ofishin babban lauyan gwamnati ya ce wasu 'yan bindiga ne suka bude wuta akan masu zanga-zanga a garin Valera dake yammacin kasar.

Edy Alejandro Teran Aguilar ya mutu a sanadiyar harbin da aka yi masa a kirjinsa, kuma mutane biyu sun jikkata.

Masu zanga-zangar da suke bukatar shugaba Maduro ya sauka daga mulki, kuma ya gudanar da zabe, sun fita titunan kasar ranar Asabar, ranar ta 50 da fara zanga-zangar da ta mamaye yankunan kasar a makonnin da suka gabata.

An kiyasta cewa an raunata mutane 46 a lokacin wannan zanga-zangar a gabashin birnin Caracas, wurin da aka kai ma Mista Figuera mai shekaru 21 da haihuwa wannan harin.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wani dan jarida kuma dan siyasa, Mista Earle Herrera yana cewa ana tuhumar mutumin ne da yin sata.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ga wuta na cin Orlando José Figuera
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai mutumin asibiti bayan da aka kashe wutar, kuma ta kona kashi 80 cikin dari na jikinsa

Labarai masu alaka