Kwastam sun kama ɗaruruwan manyan bindigogi a Lagos

Bindigogin da kwastam ta kwace Hakkin mallakar hoto Nigeria Customs
Image caption Ba wannan ne karon farko da Hukumar Kwastam ke kama makamai a tashar ruwan Legas ba

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya wato (Kwastam), ta ce ta kama manyan bindigoyi da wasu mutane suka yi yunƙurin shiga da su ƙasar a boye.

Shugaban hukumar mai kula da tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island a Legas, Bashir Yusuf, ya shaida wa BBC cewa wata kwantena ce aka kama makare da bindigogi 440.

Ya kara da cewa an shigo da makaman ne sanfurin Pump-action daga kasar Turkiyya.

Kuma kawo yanzu hukumar ta cafke mutum guda da ake zargi da hannu wurin shigo da makaman.

Babu cikakken bayani kawo yanzu kan ko makaman na wane ne, kuma ko'ina aka nufa da su.

Wannan kame, wanda ba shi ne irinsa na farko ba, ka iya tayar da hankulan 'yan kasar ganin halin rashin tsaron da ake fama da shi.

Najeriya dai tana fama da rikicin 'yan tayar-da-ƙayar-baya a yankin Arewa maso Gabashi da kuma masu fasa bututan man fetur a yankin Neja-Delta mai arziƙin mai.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Customs
Hakkin mallakar hoto Nigeria Customs

Labarai masu alaka