Giwa ta kashe mafarauci a Zimbabwe

Al'amarin ya faru ne kusa da gandun daji na Zimbabwe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Al'amarin ya faru ne kusa da gandun daji na Zimbabwe

Wani mafaraucin namun daji ya mutu sakamakon murtsuke shi da giwa ta yi a kusa da wani gandun daji a Zimbabwe.

Kafar yada labarai ta Afrika Ta Kudu News24, ta ruwaito cewa hakan ya faru ne sakamakon harbin giwar da aka yi.

Mai magana da yawun gandun dajin na Zimbabwe Mr Simukai Nyasha, ya shaida wa jaridar Telegraph ta birtaniya cewa, mafaraucin mai suna Theunis Botha, mai shekara 51, yana jagorantar tawagar mafarauta ne sai kwatsam suka samu kansu cikin tsakiyar giwaye.

Wani mutum da ba ya so a ambaci sunansa ya shaida wa tashar News24 cewa, daya daga cikin mafarautan ne ya harbe giwar bayan da ta kanannade Mista Botha da hancinta ta daga shi sama.

Tashar News24 ta kara da cewa, harbin giwar ya zo ne bisa tsautsayi, don haka a lokacin da giwar ta fadi kasa warwas, sai ta fada kan Mista Botha.

Labarai masu alaka