An kama mutum 141 a liyafar 'yan luwadi a Indonesia

Ba a haramta luwadi ba a Jakarta amma 'yan sanda sun ce za a tuhumi mutanen karkashin dokar da ta haramta batsa Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ba a haramta luwadi ba a Jakarta amma 'yan sanda sun ce za a tuhumi mutanen karkashin dokar da ta haramta batsa

'Yan sanda a Indonesiya sun kama mutum 141 wadanda suka halarci wata liyafa da suka kira ta da suna 'walimar 'yan luwadi,' a Jakarta babban birnin kasar a ranar Lahadi.

'Yan sanda sun ce wadanda suka halarci liyafar sun hada da wani dan BIrtaniya da dan Indonesiya, sun kuma biya dala 10 don su halarci liyafar.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar matsin lamba ga 'yan madigo da luwadi wadanda ba su da yawa sosai a kasar.

A karkashin dokar Indonesiya dai ba a haramta luwadi ba, sai a yankin Aceh kawai.

Amma mai magana da yawun 'yan sandan Jakarta Raden Argo Yuwono, ya ce za a tuhumi wasu daga cikin mutanen da aka kama din a karkashin dokokin kasar da suka haramta batsa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A yankin Aceh ne kawai aka haramta luwadi a kasar
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A farkon watan nan 'yan sanda sun yi irin wannan kamen a birnin Surabaya

Ya shaida wa BBC cewa, "Akwai 'yan luwadin da aka kama su tsirara suna kuma tattaba jikinsu da nufin jin dadi."

A karkashin dokar dai, ana ganin nuna tsiraici ko gamsar da kai a matsayin batsa.

A makon da ya gabata ne, aka yi wa wasu mutane biyu bulala a bainar jama'a bayan da aka kama su suna luwadi, karon farko da aka yi irin wannan hukunci tun bayan gabatar da dokar a shekarar 2014.

A farkon watan nan ne, 'yan sandan kasar suka kama mutum 14 a birnin Surabaya saboda hada wata liyafar luwadi. Su ma za su fuskanci tuhuma karkashin dokokin da suka haramta batsa.

Labarai masu alaka