An ƙona sassan jikin dabbobin daji 4,400 a Nepal

Sassan jikin dabbobi Hakkin mallakar hoto ISHWOR JOSHI/BBC
Image caption An kona sassan jikin matattun dabbobi

Hukumomin kasar Nepal sun kone sassan jikin dabbobi sama da 4,000 a kokarinsu na hana yin farauta da kuma sayar da namun daji ba bisa ka'ida ba.

Kahon karkanda, da fatun damisa, na cikin abun da aka fi konawa ranar Litinin a gidan namun dajin Chitwan, da ke kudancin Kathmandu.

Ministan harkokin waje Prakash Sharan Mahat ne, ya tsara kone sassan jikin namun dajin a gidan namun daji na kasar, inda ake a jiye mafi yawan miyagun namun daji na duniya, don ya nuna muhimmancin ranar wayar da kan jama'a a kan dabbobi.

"Muna fatan kone fatun matattun namun dajin zai taimaka wajen isar da sakon cewa, sassan jikin nasu na da amfani ne kawai idan suna raye, matukar ba sa raye ba su da wani sauran amfani," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto MAHESH ACHARYA/BBC
Hakkin mallakar hoto ISHWOR JOSHI/BBC
Hakkin mallakar hoto ISHWOR JOSHI/BBC

Maheshwar Dhakal tare da sakataren hukumar kula da gandun daji sun shaida wa BBC cewa, Hakan zai kawo karshen hana cinikin sassan dabbobin ba bisa ka'ida ba.

Mista Dhakal ya ce, "Babu hikimar kashe makudan kudi wajen kula da adana abun da a karshe zai lalace."

Bayanan da gwamnati ta tattara sun nuna cewa, kasar Nepal na da damisa 198 da karkanda 645 a yanzu, idan aka kwatanta da shekaru da dama da suka shude inda a lokacin take da damisa 91 da karkanda 372.

Hakkin mallakar hoto ISHWOR JOSHI/BBC

Jami'ai sun yi amanna cewa, daukar tsattsauran matakai a kan haramtacciyar farauta, da hukumar kula da gandun daji, da kuma kara wayar da kan jama'a na cikin abubuwan da za su kawo nasara.

Kafin a fara kone-konen an ga kwarankwal din barewa da wasu jakunkunan kayayyaki, sai dai jami'ai sun bayar da shawarar cewa, kada a konahauren giwa da suka haura kilo giram 1,100.

Hakkin mallakar hoto MAHESH ACHARYA/BBC
Hakkin mallakar hoto ISHWOR JOSHI/BBC

Labarai masu alaka