Matar Malam Aminu Kano ta rasu

Hajiya Shatu ta mutu ta bar jikoki da dama amma ba sauran 'ya'yanta da suke a raye Hakkin mallakar hoto DailyNigerian
Image caption Hajiya Shatu ta mutu ta bar jikoki da dama amma ba sauran 'ya'yanta da suke a raye

A ranar Litinin ne mai dakin shahararren dan siyasar nan a jamhuriyya ta farko da ta biyu, Malam Aminu Kano ta rasu, tanada shekara 80.

Hajiya Shatu Aminu Kano ta rasu ne bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce dumbin mutane ne suka yi ta tururuwa zuwa gidan Alhaji Sani Kabara da ke titin gidan Zoo don halartar jana'izarta.

An binne ta ne a makabartar Dandolo da ke cikin birnin Kanon.

Malam Aminu Kano dai shi ne shugaban jam'iyyar NEPU da PRP a jamhuriyya ta farko da ta biyu, kuma an san shi da kokarin kare hakkin talakawa da ci gaban arewacin Najeriya.

Labarai masu alaka