'Yan sanda sun tsinci gawa ba kai a Port Harcourt

'Yan sanda sun ce sun kaddamar da bincike Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda sun ce sun kaddamar da bincike

Da safiyar ranar Litinin ne al'ummar yankin Rumuosi da ke birnin Fatakwal a Kudancin Najeriya suka tashi da wani abin al'ajabi inda suka ga gawar wani mutum a yashe a gefen kwata ba kai sai gangar jiki.

Sun ga kan a can gefe guda da kuma adda a kusa da kan.

Zuwa yanzu dai babu dai wanda zai iya fadar yadda abin ya faru, ko yadda aka kashe mutumin ko kuma sanin wanda ya kashe shi.

Tuni 'yan sandan birnin Fatakwal din suka kai gawar mutumin mutuware, sun kuma tabbatar da kisan tare da kadamar da bincike a kan lamarin.

Za a binciki yadda 'yan sanda suka 'gallazawa' wani mutum

'Sai 'yan sanda sun sani za ka yi budurwa'

Sai dai sun ce ba su gano ko waye ya aikata kisan ba, amma sun ce da alama mutumin da aka kashe din na dawowa ne daga gona a lokacin da aka kai masa hari.

Sun ce kisan ya yi kama da irin wanda 'yan kungiyar asiri ke yi.

Dama dai birnin Fatakwal ya yi kaurin suna wajen kashe-kashen da suke da alaka da kungiyar asiri da kuma ayyukan masu tayar da kayar baya.