Me ya sa ake kashe mata a Afirka ta Kudu?

Karabo Mokoena Hakkin mallakar hoto KAYFAB_27
Image caption Mutuwar matar mai shekara 22 da haihuwa, yana zama kisan gilla na baya-bayan nan da ake yi wa mata, batun da ke daukar hankula jama'a

An dauko gawar Karabo Mokoena a wata farar karaga. 'Yan uwanta da abokanta sun taru domin yin bankwana da ita.

An tsinci gawarta wacce har ta fara lalacewa, a cikin wani kabari maras zurfi a wani fili, kwanaki masu yawa bayan bacewarta.

Ana zargin saurayinta mai suna Sandile Mantsoe ne ya kasheta, ya sanya wa gawarta sinadarin acid, domin kawai ta yi barazanar rabuwa da shi.

Ana tuhumar Mista Mantsoe da laifin kisan kai, tare da keta shari'a, amma bai amsa laifinsa ba.

Mutuwar matar mai shekara 22 da haihuwa, yana zama kisan gilla na baya-bayan nan da ake yi wa mata, batun da ke daukar hankulan jama'a.

An dai birne ta a garin Soweto da ke birnin Johannesburg.

Adele Tjale, daya daga cikin dubban mutanen da suka halarci wurin bizne Karabo ta bayyana fushinta game da mutuwar.

Shugaba ce a cocin da Mis Mokoena ke halarta, wadda take "uwa a addinance" ga marigayiyar.

Cikin fushi tare da hawaye a fuskarta, misis Tjale ta ce, "Na fusata, bai kamata wannan abu ya zama ruwan dare ba, 'yan mata da yawa na mutuwa....shugabannin wannan kasar sun gaza kare 'ya'ya mata.

Tun bayan da aka tsinci gawar Mis Mokoena, an gano gawarwakin wasu mata hudu a sassa daban-daban na kasar - wadanda suma an yi masu kisan gilla ne.

Kashe-kashen sun jawo muhawarori masu zafi a shafukan sada zumunta. Mata sun rika amfani da maudu'in #MenAreTrash don yada labaran cin zarafin mata.

'Da ban yi tsalle ba, da mutuwa nayi'

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Kasar Afirka Ta Kudu ke da alkaluma mafi yawa wajen laifun cin zarafin mata

Lamarin dai ya jayo ce-ce-ku-ce a kan mace-macen mata da ke faruwa. Daya daga ciki labaran da ya dauki hankali shi ne na Bukelwa Moerane.

Wata rana a watan Fabrairu tana kan hanyarta ta dawowa daga kasuwa - wani, wanda bata san ko wane ne ba, ya sace ta a cikin motar tasi.

"Wani mutum ne ya lababo ta bayana, ya tilasta min shiga motarsa," in ji matar 'yar shekara 24, wadda har ta rasa hakoranta da samun raunukan da suka razana ta matuka.

"Ya yi ta zagina, yana kirana da sunayen banza, yana cewa sai ya yi min fyade kuma zai kasheni".

"Na sani dole in nema wa kaina mafita," ta bayyana min, tana yi tana mutsuka 'yan yatsunta.

Mis Moerane ta zabi ta yi tsalle daga cikin motar duk da tana gudu, ta yi gudun wasu kilomitoci domin neman taimako.

Amma ba wanda aka kama kan lamarin.

"Da ban yi tsallen ba, na san mutuwa zan yi. Amma gara in mutu cikin kokarin kare rayuwata," in ji ta, tana zubar da hawaye.

Shugaba Jacob Zuma ya bayyana "wannan batu na kisan mata da kananan yara" a matsayin wani "babban rikici da kasar ke fuskanta".

Ya umarci wadanda aka ci zarafinsu da kar su bar lamarin ya wuce. Ya kuma ce zai duba kiraye-kirayen da ake yi masa na tabbatar da hukunci mai tsanani ga masu cin zarafin mata.

Wani bincike da kungiyar Statistics SA ta byi a 2016, ya nuna cewa kowace mace daya cikin mata biyar na fuskantar cin zarafi daga abokin zamanta.

Haka kuma binciken ya nuna kashi takwas cikin dari na mata sun fuskanci cin zarafi a cikin wata 12 da suka gabata, yayin da kashi shida cikin dari sun fuskanci cin zarafin daga hannun abokin zamanta.

Labarai masu alaka