Ko ƙayyade iyali na taimakawa bunƙasar tattalin arziki?

kwayoyin kayyade iyali Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata a Amurka sun fara amfani da ƙwayoyin ƙayyade iyali wajen yin karatu mai zurfi

Margaret Sanger, wata mai fafutikar ƙayyade iyali, wadda kuma ta umarci likitoci su tabbatar da shi, na son a bai wa mata hakkinsu ta bangaren zamantakew da rayuwa daidaita da abokan rayuwarsu maza.

Ana ganin kwayoyin kayyade iyali a matsayin abin da ya yi tasiri sosai ba ta fuskar sauya rayuwar jama'a ba kawai, har ma ta taimakawa wajen habakar tattalin arzikin duniya a karni na 20.

Shekaru aru-aru da suka shude, masoya na amfani da magunguna daban-daban wajen hana daukar ciki.

Akwai tsofaffin hanyoyin han daukar ciki kamar wadda Aristotle ya kawo ta amfani da man "cedar", da kuma hanyar da Casanova ya bullo da ita, ta amfani da lemon tsami.

Hatta, ita kanta sabuwar hanyar da aka bullo da ita ta amfani da kwaroron-roba tana da nata nakasu.

Saboda mutane ba sa amfani da shi yadda ya kamata, wani lokaci su kan huda shi ko su yaga shi ba tare da sun sani ba.

Saboda haka cikin mata 100 da suke amfani da kwaroron-roba a shekara, a kan samu 18 daga cikinsu su dauki ciki.

Bunkasar tattalin arziki

Amfani da kwaroron-roba na nufin mu'amala da abokin hulda, ta yadda kwayoyin halittar juna ba za su hadu da juna ba.

Amma matakin amfani da kwayoyi, abu ne na daban kuma mata sun sun fi son amfani da wannan hanya fiye da kowacce.

Image caption Amma a shekarun 1970, shekara 10 bayan an amince da amfani da kwayoyi

Magungunan an fara amfani da su ne a kasar Amurka a shekarar 1960. A shekaru biyar da aka fara amfani da su, matan aure da ke bukatar kayyade iyali ne suka fara amfani da su.

Amma tabbataccen sauyi ya zo ne lokacin da mata marasa aure suka fara samun wadannan kwayoyi. Wannan ya dauki lokaci mai tsawo.

Amma a shekarun 1970, shekara 10 bayan an amince da amfani da kwayoyin, Amurka ta fara saukaka samun kwayoyin ga matan.

Ci gaba ta fuskar kwarewa

Jami'o'i sun bude cibiyoyin kayyade iyali. A tsakiyar shekarun 1970, kwayoyin sun zama, wasu sanannun kwayoyi tsakanin mata masu shekara 19 zuwa 18 a kasar Amurka.

Mata a Amurka sun fara karantar fannonin Shari'a, da likitanci, da harkar sanin magunguna a jami'o'i, wadanda da a baya fannoni ne da maza suka mamaye.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption mata sun fara karantar fannonin Likitanci a jami'o'i, saboda kwayoyin kayyade iyali

Amma a farko-farkon shekarun 1970 mata sun fara karantar wadannan kwasa-kwasan, saboda samun kwayoyin hana haihuwa, matan sun zama kashi daya cikin biyar na masu karantar kwasa-kwasan, daga baya suka dawo kashi daya cikin hudu, amma a shekarar 1980 sun zama kashi daya cikin uku.

Mata da ke sha'awar karatu sun fara karanta wadannan kwasa-kwasai.

Amma kuma me wannan yake nufi? Bai wa mata kwayoyin kayyade haihuwa, kan taimaka musu wajen cimma burinsu a rayuwa.

Zamantakewar auratayya

Hakika mata su na iya gujewa jima'i idan suna so su yi karatu don kwarewa a wani fanni. Amma da yawa ba sa son yin hakan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption kafin samun wadannan kwayoyi mata kan yi aure da wuri

Kafin samun wadannan kwayoyi, mutane su kan yi aure da wauri. Matar da ke bukatar yin karatu mai zurfi kan yi aure lokacin da ta kai shekara 30, kuma kafin ta kai lokacin, duk an zabe mazan masu halin.

A kasar Japan, wacce take daya daga cikin manyan kasashen duniya da suka bunkasa ta fuskar fasaha, matan Japan su kan tsaya har tsawon shekara 39 fiye da 'yan uwansu na Amurka.

Karuwar samun kudi?

Al'amura da dama sun faru a shekarun nan da ake kallon su a ci gaba, kamar halatta zubar da ciki, an samar da dokokin da ke adawa da nuna wariyar jinsi, an fara fafutukar kare hakkin mata, sannan kuma sanya maza matasa cikin rundunar soji a Vietnam ya sa mata da dama sun samu ayyukan yi a kasar.

Amma wani nazari da wasu malamai a jami'ar Havard suka yi Claudia Goldin da Lawrence Katz, ya ce lallai amfani da kwayoyin kayyade iyali ya taka babbar rawa wajen sanya mata su ki yin aure da wuri ko su ki haihuwa da wuri ko kuma su fara gina rayuwarsu wajen kokarin neman na kai.

Labarai masu alaka