Nigeria ta ce za ta binciki rikicin 'yan Shi'a na 2015

Harkokin tsaron Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnati za ta bincike rikicin 'yan Shi'a da na Biafra in ji Ministan tsaro na Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta yi alƙawarin ƙaddamar da bincike kan zarge-zargen keta haƙƙoƙin ɗan'adam da ake yi wa jami'an tsaron ƙasar ciki har da rikicin Zaria tsakanin sojoji da mabiya Sheikh El- Zakzaky na shekara ta 2015.

Ministan tsaron ƙasar, Janar Mansur Muhammad Ɗan Ali mai murabus ya ce za a naɗa wani alƙali da zai jagoranci bincike kan abin da ya faru a Zaria, da kuma na Biafra, da na Arewa maso Gabas.

"Za a duba kowanne ɓangare, a duba laifin da kowa a aikata don a yi wa kowa hukunci daidai da irin laifukan da suka aikata."

Ministan tsaron ya ce "akwai kotu-kotu da muke son mu kafa inda za a samu alƙali da zai saurari duk waɗannan abubuwa da suka faru.

Al'amuran da aka yi irin na Zariya da na mutanen da ke rajin kafa ƙsar Biafra masu neman ɓallewa da ma can arewa maso gabas.

Muna sa zato in wannan kwamiti da zai ƙunshi zaɓaɓɓun lauyoyi da waɗansu 'yan Nijeriya da za su zauna su ba kowanne ɓangre laifinsa."

A baya dai, gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin bin bahasi kan abin da ya faru tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya.

Kwamitin ya gano abubuwa da dama da suka hada da aikata kisa da binne mabiya mazhabar Shi'a 347 a wasu maka-makan ramuka na bai ɗaya.

Haka zalika, ya ba da shawarar hukunta jami'an tsaron da suka aiwatar da kisan 'yan Shi'a a Zariyar da haramta kungiyar 'yan uwa musulmi ta IMN tare kuma da hukunta shugabanta, El-Zakzaky.

Ya ce ya buɗe wani ofis takanas a shalkwatar tsaro, wanda yake nazari kan irin waɗannan zarge-zarge na keta haƙƙin ɗan'adam.

Sai dai ministan bai bayyana lokacin da wannan kwamiti ko kotu da ya ambata za ta fara gudanar da aikin ba.

Hukumomin kare haƙƙin ɗan'adam dai sun sha zargin dakarun tsaron Nijeriya da tafka ayyukan keta haƙƙin ɗan'adam, zargin da hukumomi suka sha musantawa.

Ministan tsaro Mansur Ɗan Ali dai ya bai wa al'umma tabbacin hukunta duk wanda aka samu da laifi kan aikata irin wadannan ayyuka.

Labarai masu alaka