Ɗan ƙunar baƙin wake ne ya kai hari gidan rawa a Manchester

Birnin Manchester na Ingila Hakkin mallakar hoto PETER BYRNE
Image caption Jami'an 'yan sanda na sintiri a wurin dake tsakiyar birnin na Manchester, wanda aka riga aka kewaye

'Yan sanda a birnin Manchester na Ingila sun ce mutum 22 sun hallaka, kusan 60 kuma sun ji munanan raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a cibiyar raye-raye ta Manchester Arena.

Sun kuma danganta faruwar lamarin da mai yiwuwa, ayyukan ta'addanci.

'Yan sandan sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya dasa bam kuma shi ma ya mutu a harin.

Fashe-fashen sun auku ne jim kaɗan bayan wata mawakiya 'yar Amurka Ariana Grande, ta kammala cashewa a makeken gidan raye-rayen.

Wani ganau ya faɗa wa BBC cewa babbar fashewar ta yi jifa da shi har zuwa tsawon mitoci da dama.

Ta kuma jijjiga gine-gine, tare da yin watsi da karikicen karfe da gilasai zuwa sama.

Shaidar ya ce ya iya ganin yadda mutane da dama suka yi kwance magashiyan a ƙasa, nan take wasu suka mutu.

Kwararru a fannin kwance bama-bamai da 'yan sanda na ta sintiri a wurin da ke tsakiyar birnin Manchester, wanda aka riga aka killace.

An kuma rufe tashar jirgin ƙasa da Manchester Victoria, wadda ke daf da wurin da lamarin ya faru, tare da dakatar da zirga-zirgar ɗaukacin jiragen kasa a yankin.

Firai ministar kasar ta kira taron gaggawa a kan lamarin, kuma an sa ran za ta kai ziyara birnin Manchester zuwa an jima.

Image caption Olivia Campbell 'yar shekara 15 ta bata tun lokacin da abin ya faru

Wani babban jami'in 'yan sandan ya ce, lamarin shi ne abu mafi firgitarwa da birnin ya taba fuskanta.

Ya ce a yanzu haka ana binciken gaggawa don a gano ko dan kunar bakin waken shi kadai ne ko kuma yana aiki ne da wasu gungun mutanen daban.

Tuni mutane sun sanya cigiyar 'yan uwansu a shafukan sada zumunta, kuma an samar da lambar gaggauwa ta kiran hukumomi.

Motocin daukar marasa lafiya 60 ne suka hallara a wajen don daukar mutane zuwa asibiti.

Shaidu sun ce sun ji fashewar wani abu har sau biyu a kusa da ofishin sayen tikitin shiga cibiyar raye-raye ta Mancheter Arena.

Kuma hakan ya faru ne a daidai lokacin da 'yan kallo da dama suka maƙare a katafaren zauren dafdalar.

A shafinta na Twitter, rundunar 'yan sanda ta Manchester ta yi gargadi tare da yin kira ga jama'a su janye jiki daga yankin.

Mutane da dama sun bayyana irin rudanin da suka shiga bayan faruwar lamarin.

Robert Tempkin, mai shekara 22, daga yankin Middlesbrough ya ce; ''Mutane sun yi ta ihu cikin halin ɗimauta, suna da guje-guje, yayin da ake iya ganin wayoyin salula da rigunan kwat da sauran kayan mutane yashe a kasa.''

Michelle Sullivan, daga yankin Huddersfield, ta halarci wurin rawar da 'yayanta mata biyu 'yan shekara 12 da 15, ta ce " Abin da ban tsoro, jim kadan bayan daukewar wutar lantarki sai muka ji wata irin ƙara...kowa sai ihu yake.''

"Lokacin da muka fita, sun ce mana mu yi ta gudu.''

Labarai masu alaka