Tsohuwar shugabar Korea ta Kudu ta gurfana a gaban kotu

Korea ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ms. Park da aminiyarta, Choi Soon-Sil na fuskantar tuhume-tuhumen tozarta mulki da karɓar cin hanci.

An gurfanar da tsohuwar shugabar Koriya ta Kudu, Park Geun Hye gaban kotu a Seoul babban birnin ƙasar bisa zarge-zargen cin hanci.

Karon farko kenan da aka gan ta a bainar jama'a tun bayan tsige ta daga mulki tare da kamun da aka yi mata a watan Maris.

Ms. Park da aminiyarta, Choi Soon-Sil na fuskantar tuhume-tuhumen tozarta mulki da karɓar cin hanci.

Masu shigar da ƙara sun ce mutanen biyu sun kafa ƙahon zuƙa ga kamfanoni ta hanyar karɓar kuɗi a matsayin gudunmawa, amma suka riƙa karkatarwa don amfanin kai.

Sai dai tsohuwar shugabar da aminiyar tata sun musanta zarge-zargen.

Labarai masu alaka