Burtaniya ta biya James Ibori diyyar fam

An daure James Ibori a gidan yari a shekarar 2012 kan laifukan da suka danganci almundahana Hakkin mallakar hoto Metropolitan Police
Image caption An daure James Ibori a gidan yari a shekarar 2012 kan laifukan da suka danganci almundahana

Kotu ta bayar da umarnin a bai wa James Ibori diyyar fam daya, kwatankwacin naira 450, saboda tsare shi da aka yi ba bisa ka'ida ba har tsawon wa 24 a Burtaniya.

James Ibori dai tsohon gwamnan jihar Delta ne mai arzikin mai da ke Kudancin kasar, wanda aka same shi da laifin almundahana.

Ya kamata a sake shi ranar 209 ga watan Disambar 2016, amma maimakon haka sai jami'an shige da ficen Birtaniya suka tsare shi.

Bayan an sake shi ne ya kai sakatariyar harkokin cikin gida ta Burtaniya Amber Rudd kara yana neman diyya saboda tsare shi ba bisa ka'ida ba da kuma tauye hakkokinsa.

A ranar Litinin ne mai shari'a Cheema-Grubb, ta ce sakatariyar harkokin cikin gidan ta aikata ba daidai ba a daukacin huldar da ta yi da Mista Ibori a makonnin da suka gabaci sakin sa, don haka a ganinta an tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Sai dai kuma ta ki amincewa da bukatar Mista Ibori ta cewa a ba shi diyyar fam 4,000. A maimakon haka sai ta bayar da umarnin a ba shi diyar fam daya kacal.

Mai shari'ar ta kuma ce mai yiwuwa an yanke shawarar tsare shi ne saboda miliyoyin fama-faman da hukumomi ba su kwace daga hannunsa ba.

Wani sakon email da aka ambata daga hukumar harkokin cikin gida, ya bayar da shawarar ajiye shi wajen jami'an shige da fice don a samu damar gano wata dabara da za a yi amfani da ita don karbar a kalla fam miliyan 57 a hannunsa.

A ranar 21 ga watan Disambar 2016 ne alkalin wata babbar kotu ya bayar da umarnin a sake shi daga gidan yari ba tare da bata lokaci ba. Mista Ibori ya bar Burtaniya a watan Fabrairun 2017.

Hakkin mallakar hoto Metropolitan Police
Image caption Daya daga cikin kadarorin da James Ibori ya mallaka a London wanda aka saya kan kudi fam miliyan 2.2

Waye James Ibori?

Dama dai an taba zargin James Ibori da laifin sata kafin ya zama gwamna, daga baya kuma sai ya zama gwamna, sannan aka tuhume shi da laifin halatta kudin haram.

Ya je Burtaniya ne a shekarun 1980 ya kuma yi aiki a matsayin akawu a kantin DIY da ke London.

An kama shi a shekarar 1991 da laifin sata a kantin, amma daga baya ya koma Najeriya ya shiga harkokin siyasa.

Ya zama gwamna a shekarar 1999 daga nan ne kuma aka yi zargin ya fara 'almundahana' da kudin gwamnati.

A shekarar 2005 ne 'yan sandan Burtaniya suka sake kama Mista Ibori bayan sun gano wani cinikin jirgin sama da ya yi a London.

Ya kaucewa kamun da aka so yi masa a Najeriya bayan gungun magoya bayansa sun kai wa 'yan sanda hari, amma sai aka sake kama shi a Dubai a shekarar 2010 aka kuma mika shi ga Burtaniya.