Maharin Manchester dan kwaya ne — Abokai

Harin birnin Manchester Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harin na ranar Litinin shine mafi muni da aka taba samu a birnin Manchester

Ta dai tabbata cewa maharin da ya tarwatsa kansa a gidan raye-rayen Manchester, Salman Abedi ya koma Burtaniya ne daga ƙetare, kwanaki ƙalilan kafin ya kai wannan farmaki.

Matashin mai shekara 22 haifaffen birnin Manchester ne, ɗan asalin Libya kuma an yi imani iyayensa sun koma ƙasarsu bayan zama na tsawon shekaru.

Salman Abedi ya yi makaranta a Manchester har ma ya je Jami'ar Salford da ke kusa amma ya watsar.

Abokansa na tuna shi da cewa gwanin ɗan ƙwallon ƙafa ne amma yana tu'ammali da ƙwaya.

Fira ministar Burtaniya Theresa May ta ce akwai yiwuwar gungun wasu ɗaiɗaiku na da hannu a harin maryacen ranar Litinin da aka kai gidan raye-raye na Manchester.

Ta ce Burtaniya za ta tura sojoji don tsare muhimman wurare da tarukan jama'a bayan harin ƙunar-baƙin-wake da ya yi sanadin mutuwar mutum 22.

Mrs May ce ta bayyana wannan matakin na ba-safai-ba bayan ta sanar da ɗaga ma'aunin hukuma kan barazanar ta'addancin da Burtaniya ke fuskanta zuwa matakin la'ila-ha'ula'i.

Hakan dai na nufin mai yiwuwa ne a samu ƙarin wasu hare-hare a nan gaba.

Labarai masu alaka