An shiga halin la'ilaha ula'i a ƙasar Burtaniya

Theresa May
Image caption Theresa May ta ce za a tura sojoji muhimman wurare don kare rayukan al'umma

Burtaniya za ta tura ɗaruruwan sojoji don tallafa wa 'yan sanda, yayin da gwamnati ke gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun ƙarin hare-hare.

Hukumomi sun ɗaga mizanin barazanar harin ta'addanci zuwa matakin la'ilaha ula'i, mafi ƙololuwa a cikin shekara goma

Fira ministar Burtaniya Theresa May ta ce ƙasar ta ƙure mizanin barazanar kai mata harin ta'addanci a yanzu.

Ta ce matakin ya zo ne bayan masu bincike sun gaza tsaida hukunci a kan ko matashin da ake zargi da kai harin bam a Manchester, Salman Abedi shi kaɗai ya shirya abinsa.

A yanzu za a tura dakarun soja don kare muhimman wurare a ƙasar.

'Yan sanda sun ce sun gudanar da bincike birjik a wani ɓangare na wani bincike mai saurin gaske kuma sun ce suna samun kyakkyawan ci gaba.

Mutum 22 ne suka mutu wasu 59 kuma suka ji raunuka lokacin da wani ɗan harin ƙunar-baƙin-wake ya far wa gidan raye-raye na Manchester Arena da maraicen ranar Litinin.

Fira minista May ta kuma tabbatar cewa gwamnati ta bijiro da wani shirin soja na gaggawa mai taken "Operation Temperer", inda za a jibge dakarun ƙasar a muhimman fuskokin gari don tallafa wa 'yan sanda wajen kare al'umma.

Haka zalika, ana iya ganin sojoji a wasu tarukan jama'a cikin makwanni masu zuwa ciki har da gidajen raye-raye, in ji ta. Ko da yake, za su yi aiki ne a ƙarƙashin ikon jami'an 'yan sanda.

Image caption Saffie Roussos 'yar shekara takwas da Georgina Callander na daga cikin mutum uku da 'yan sanda suka bayyana sunayensu a matsayin mutum 22 da harin ya hallaka

Fira ministar ta ce ba ta son mutane su cika da "fargaba kan abin da bai kai ya kawo ba" amma a cewarta abin da gwamnati ta yi shi ne "ya dace kuma yana cikin hankali da halin da ake ciki".

Ta ce gwamnati za ta ɗauki "duk wani mataki da za ta iya" don taimakawa 'yan sanda kare al'umma.

"Ƙarfin halin al'ummar Manchester da na Burtaniya ya fi ƙarfin ƙeƙasasshiyar maƙarƙashiya ta miyagun 'yan ta'adda.

"Don haka 'yan ta'adda ba za su taɓa samun nasara ba kuma mu ne da galaba a kansu," in ji ta.

Sau biyu ne kaɗai aka taɓa ƙure mizanin barzanar kai harin ta'addanci Burtaniya.

Karon farko shi ne a shekarar 2006 lokacin wani gagarumin aiki na dakatar da wata maƙarƙashiya ta tarwatsa jiragen sama da bama-bamai masu ruwan sinadarai.

Sai kuma shekarar da ta biyo baya, inda manyan jami'an tsaro suka sake ƙure mizanin lokacin da suke farautar mutanen da suka yi ƙoƙarin tayar da bam a wani gidan rawa na London, kafin su je su kai hari filin jirgin saman Glasgow.

An fahimci cewa Salman Abedi tsohon ɗalibin Jami'ar Salford mai shekara 22, haifaffen Manchester, iyayensa 'yan asalin Libya - ya tarwatsa kansa ne a zauren gidan raye-rayen lokacin da 'yan kallo suka fara fita bayan wata mawaƙiya 'yar Amurka Ariana Grande ta gama wasa.

Labarai masu alaka