Nigeria: Wanne sauyi Buhari ya samar a ɓangaren noma?

Kashi 1.6% cikin 100 kacal gwamnatin Najeriya ta ware wa harkar noma a cikin kasafin 2017 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kashi 1.6% cikin 100 kacal gwamnatin Nijeriya ta ware wa harkar noma a cikin kasafin 2017

Wanne irin tasiri hana shigar da shinkafa Najeriya ta tudu ya yi? Shin janye tallafi a kan takin zamani ya inganta noma a kasar? Wanne sauyi gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo a harkar noma? Shin ma ta soma cika alkawuran da ta dauka a fannin noma? Dakta Aliyu Tilde wani manazarci kuma kwararre kan harkar noma, ya yi nazari kan wannan batu.

Venezuela da Najeriya ƙasashe ne biyu da gwamnatocinsu suka dogara kan man fetur wajen samun kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje. Yau shekara uku ke nan tun da farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwannin duniya inda ya sauko daga $120 a 2012 har zuwa $30 a 2015.

Sai dai tasirin faɗuwar man fetur a kasashen biyu ya bambanta. Duk da akwai ƙarin matsin rayuwa a ƙasashen biyu, a Venezuela muhimman abubuwan rayuwa kamar magunguna da abinci sun gagara.

Mutane suna shafe tsawon kwanaki a layi kafin su samu abincin da za su saya su ci.

A Nijeriya, inda akasarin mutanen ƙasar manoma ne, an ci gaba da noma abinci kamar yadda aka saba. Hasali ma, a 2016 an samu amfanin gona wanda an jima ba a samu irinsa ba saboda albarkar damuna. Duk da matsin rayuwa a Nijeriya a yau, akwai magunguna da sauran muhimman abubuwan rayuwa da mutane za su saya ba kamar a Venezuela ba.

Wannan bambanci tsakanin ƙasar biyu wajen tasirin faɗuwar farashin man fetur a kan rayuwar jama'a ya samo asali ne daga cewa yayin da tattalin arziƙin Venezuela da mutanenta suka dogara kacokam a kan man fetur wanda da kuɗinsa ake shigo da abinci da sauran muhimman abubuwan more rayuwa daga ƙasashen waje, a Nijeriya noman cikin gida ne yake taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da mutanen ƙasar. Tun shekarar 1984, noma yake ba da wajen kashi 40% na arizikin mutanen kasar (GDP).

To amma duk da samun abinci a ƙasarsu, jama'ar Nijeriya na matuƙar kokawa da tsadarsa, har ta kai talakawa da yawa ba sa iya sayensa isasshe. Alal misali, buhun shinkafa mai kilo 25, ya ninka kuɗinsa daga N8,000 a 2015 zuwa N19,000 a 2016; masara - wadda ita ce talakawa suka dogara da ita - buhunta ya ninka sau uku daga N5,000 zuwa N15,000; suga shi ma daga N6,800 zuwa N19,500, da sauransu.

Da kakar bara, an samu sauƙin kayan kaɗan a inda ƙaramin buhun shinkafa ya sauko zuwa N15,000 har tsawon wata daya, amma a watan Afrilun bana farashin kayayyakin sun fara tashi kuma. A kasuwar Jos misali, bayan sauƙi da aka samu kwanan baya, a yanzu ana sayar da buhun suga a N18,500; buhun masara a N14,000; na shinkafa a N18,000. Ana kuma tsoron farashin zai ci gaba da ƙaruwa musammam idan damuna ta yi nisa.

Abubuwa biyu ne suka kawo tsadar abinci a Nijeriya: Hana shigo da shinkafa ta iyakokin tudu da kuma janye kowanne irin tallafi na aikin noma har da na takin zamani da sabuwar gwamnatin ta yi— matakai biyu waɗanɗa ba wata gwamnati a baya da ta taɓa ɗauka a ƙasar. Duk da koke-koken da 'yan ƙasa da shugabanninsu da Majalisar Dattijai suka yi a kan waɗannan matakan, gwamnatin ta yi mirsisi ta tsaya a kan bakanta don ta yi imani cewa ta haka ne kaɗai ƙasar za ta zama mai dogaro da kanta. A wannan shekarar ta 2017, hana shigo da shinkafa zai haɗa har da ta teku.

Alal haƙiƙa, an samu haɓakar noman shinkafa da alkama a Nijeriya, kuma tsadar abincin ya sa mutane da yawa da suka ga uwar-bari sun koma noma amfanin ciyar da gida musammam hatsi.

To amma tsadar kayan abinci a ƙasar za ta ci gaba da sanya talaka tagumi, musammam mai karɓar albashi wanda a yanzu abin da ake biyan shi ba zai saya masa rabin abin da yake saya masa ba shekara biyu da ta wuce, kuma ga shi gwamnati da kamfanoni sun ƙi ƙara albashi balle ma'aikatan su samu sa'ida.

A nan, ana iya tambaya: Mene ne manufofin gwamnatin a aikin noma da kiwo kuma ina ta kai wajen cim ma waɗannan manufofi?

Idan ana batun manufofin gwamnatin siyasa a duniya, ma'auni na farko shi ne a duba alƙawuran da ta yi wa mutane lokacin zaɓe sannan a haɗa da waɗanda ta yi bayan ta hau mulki. Cikin alƙawurran da ta yi, nawa ta cika?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Faduwar farashin man fetur ya sa naira ta karye

A kundin manofofi na jam'iyya mai ci a Nijeriya yanzu - wato APC - akwai alƙawari 19 da jam'iyyar ta ce za ta cika idan 'ƴan Nijeriya suka zaɓe ta a shekarar 2015.

A wajen bibiyar ina aka kwana game da waɗannan alƙawurran, wata gamayyar ƙungiya uku - watau CDD da OSSIWA da BudgIT - sun kirkiro shafin intanet na musamman mai suna Buharimeter. A ciki, ƙungiyoyin sun nuna cewa alƙawari uku ne kacal gwamnati mai ci yanzu take wani abu a kan su cikin 19 da ta yi lokacin zabe a fannin noma.

Waɗannan su ne batun canza aikin gona daga na masu ƙaramin ƙarfi zuwa noman kasuwanci na zamani, da inganta yaɗa dabarun noma, da inganta bankunan ci gaba kamarsu Bankin Noma da Bankin Masana'antu, amma ƙungiyoyin ba su da abin cewa a kan ragowar alƙawari 16 da jam'iyyar APC din ta yi yau shekara biyu kenan bayan ta hau mulki.

Wannan ba ya nufin cewa gwamnatin ba ta yi komai ba a fannin noma. Alal misali, ta samar da tsari na bai wa manoman shinkafa bashi wanda aka aiwatar a wasu jahohi ta hanyar ba da bashin kayan aiki ga manoma. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da aka samu bunƙasar noman shinkafa a jihar Kebbi misali, inda gwamnatin jihar take ikirarin an noma sama da tan miliyan guda na shinkafa a bara.

Akwai kuma batun yarjejeniya da gwamnatin Nijeriya ta cim ma tsakaninta da ƙasar Sin. A cikin wannan yarjejeniya, ƙasar Sin za ta samar wa Nijeriya na'urorin noma da kiwo iri daban-daban da kuɗinsu ya kai $4.1bn a matsayin bashi don bunƙasa aikin noma da kiwo. Wannan shiri ya yi nisa a inda ake tsammanin isowar wasu daga cikin kayan kowane lokaci daga yanzu.

Haka kuma akwai yarjejeniya da ƙasar Morocco a kan samar da takin zamani wadda ita ma ta fara aiki, inda ita ƙasar Morocco din take tallafawa masana'antun taki na cikin gida wajen samar da wadataccen taki ga manoma a farashi mai rahusa.

Har ila yau, an samu nasarar mayar da duk jami'o'in ayyukan noma ƙarƙashin Ma'aikatar Aikin Noma da Raya Karkara don tabbatar da ganin makarantun suna taka rawar da ta kamata wajen wanzar da ilmin aikin noma da bincikensa a ƙasar.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Dr. Aliyu U. Tilde manomi ne kuma manazarci

Ministan Aikin Noma da Raya Karkara, Chief Audu Ogbe, ya yi batun samar wa makiyaya matsuguni na dindindin a jihohi daban-daban na kasar inda har a shekarar 2016 ya ba da tabbacin cewa ba saniyar da za ta yi yawo nan da wata goma sha takwas. Wannan wa'adi ya wuce amma har yanzu ba a ma ƙare gardamar zartar da dokar ba a Majalisa kuma wasu jihohi da ƙungiyoyin al'ummu sun kyamaci shirin inda suke cewa ba su da dazukan da za su ware wa makiyaya. Aikin da kamar wuya don Gwamnatin ita ma ta ce ba za ta tilasta wa kowa bayar da filinsa don shirin ba.

A ƙarshe Ma'aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya ta fito da shirin wannan gwamnati na bunƙasa aikin gona kwanan nan wanda ta yi wa laƙabi da Tsarin Bunƙasa Aikin Noma na 2016-2020 - wato Agriculture Promotion Policy. Manufar shirin, kamar na gwamnatocin baya da suka wuce, shi ne ƙasar ta zama mai ci da kanta a shekarar 2020.

Nijeriya kasa ce da ke cike da duk abin da ake buƙata na bunƙasa noma: Akwai filin noma wadatacce, da ruwan sama da koguna da madatsun ruwa, da ɗumbin manoma da makiyaya. Abin da kawai ya gaza shi ne tsarin hukuma da zai tattara waɗannan abubuwa waje daya ta yadda noma da kiwo za su bunƙasa ba tare da an bar komai a hannun talakan manomi ba, ba kuma da an bar masu hannu-da-shuni sun shiga harkar sun yi kaka-gida ba.

Tabbas Nijeriya ba Venezuela ba ce saboda waɗannan ni'imomi da Allah ya yi mata. Amma manazarta da yawa na tababar himmar wannan gwamnati da waɗanda suka shude a kan noma. Farfesa Ango Abdullahi na cewa zai yi wuya gwamnati ta iya bunƙasa noma da kashi 1.2% kacal da ta warewa harkokin aikin gona a kasafin kuɗinta na 2016 ko kashi 1.6% a cikin kasafin wannan shekara ta 2017, alhali noma ne ke bai wa 'yan ƙasa kashi 40% na arziƙinsu.

Manazartan na cewa muddin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya za ta ci gaba da manufarta na janye tallafi da rashin zuba jari a harkar noma ta bar talaka kowa tasa ta fisshe shi, to fa tsadar abinci a ƙasar ba za ta ƙare ba kuma ga akasarin yan ƙasar, wata miyar, sai dai su ji a maƙwabta.

Dr. Aliyu U. Tilde, ya yi bincike mai zurfi sannan ya rubuta wannan sharhi.

14 Maris, 2017