Muhammadu Buhari: Ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

Rashin lafiyar Shugaba Buhari ta jawo tafiyar hawainiya a aiwatar da al'amuran gwamnati Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu na ganin rashin lafiyar Shugaba Buhari ta jawo tafiyar hawainiya a aiwatar da al'amuran gwamnati

Shekara biyun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yana mulki ba su isa a yanke hukunci ba, idan ana son yin adalci, domin shugaban ya shiga fama da rashin lafiya tun wata biyar da ya gabata.

Shugaban ya yi kwana 49 a Landan, daga watan Janairu zuwa Maris, kuma bai yi wasu ayyuka masu yawa ba a watannin Maris zuwa Mayu, sannan ya koma Burtaniya a farkon wannan watan don ƙara neman lafiya. Babu wanda ya san ranar da zai dawo.

A ragowar wata 19 da Buhari ya yi mulki kuwa, gwamnatinsa ta ɓata lokaci wajen naɗa manyan jami'an da za su tafiyar da ayyukan gwamnati ne. Misali, an shafe tsawon wata uku kafin naɗa Sakataren Gwamnatin Tarayya da shugaban ma'aikatan ofishin shugaban ƙasa.

Kuma sai a watan Nuwamban 2015 ne ya naɗa ministocinsa. Hakazalika, ya ɓata wasu watannin kafin ya fara sauya shugabannin ma'aikatun da ya gada daga gwamnatin Goodluck Jonathan. Zuwa yanzu, yawancin ma'aikatu ba su da kwamitocin gudanarwa. Idan aka duba batun ma'aikata, Shugaba Buhari mai tafiyar hawainiya ne.

Buhari ya samu yawancin nasarori a shekarar 2016. Mafi muhimmanci su ne yaƙi da ƙungiyar Boko Haram, da yaƙi da cin hanci da rashawa. Duk da ƙwato yawancin yankuna da garuruwan da ƙungiyar ta Boko Haram ta mamaye a ƙarshen mulkin tsohon Shugaba Jonathan, ƙungiyar na da sauran karfinta lokacin da Buhari ya karɓi mulki.

Zuwa ƙarshen shekarar 2016, an karya lagon ƙungiyar. Akwai dalilai masu dama da suka taimaki Buhari samun wannan nasarar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabbin hafsoshin sojin da Buhari ya nada sun taimaka wajen yaki da Boko Haram

Na farko shi ne, Buhari ya san illar ƙungiyar Boko Haram, kuma bai yi kuskuren da tsohon Shugaba Jonathan ya yi ba na cewa wasu ne suke son yi wa gwamnatinsa zagon-ƙasa.

Na biyu, Buhari ya dakatar da badaƙalar sayen kayan yaƙi, kuma ya samar da makaman yaƙi ga sojojin ƙasar.

Na uku, Buhari ya naɗa sabbin manyan hafsoshin sojin ƙasar. Shugaban sojojin ƙasa Laftanal-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya kawo sabbin dabarun yaƙi da suka yi tasiri kuma ya zama abin alfahari.

Air Marshal Sadik Abubakar, babban hafsan sojin sama na Najeriya, shi ma ya ɗauki matakan da suka durƙusar da ƙungiyar Boko Haram.

Akwai kuma umarnin da Buharin ya bai wa manyan hafsoshin sojin kasar na su koma Maiduguri domin su kasance kusa da fagen daga.

Da ƙarshe ya yi nasarar samun haɗin kan ƙasashen da ke maƙwabtaka da Najeriya kamar Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin. Waɗannan matakan sun taimaka wajen ƙwato dajin Sambisa a watan Disamba.

Yaƙi da cin hanci

Fage na biyu da Shugaba Buhari ya samu babbar nasara shi ne yaƙi da cin hanci da rashawa. Wannan yaƙin ya ƙara tabbatar da farin jininsa a sassa daban-daban na ƙasar.

A karon farko, Najeriya ta yi sa'ar shugaba mai gaskiya da rikon amana. Wannan kawai ya taimaka wajen tara biliyoyin dalolin Amurka a baitul-malin ƙasar domin babu yadda za a sace arziƙin ƙasa ba tare da sanin shugaban ƙasa ba.

A ƙarƙashin Buhari, hukumomin yaƙi da rashawa irinsu EFCC sun samu ƙarfin zartar da ayyukansu, abin da ya sa suka gano kuɗaɗe masu yawa da aka ɓoye.

Binciken da Buhari ya bayar da umarnin a yi, ya sa an gano biliyoyin dalolin da aka sace lokacin tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki.

An gano cewa maimakon sayen makamai don yaƙar ƙungiyar Boko Haram, an karkatar da biliyoyin naira, waɗanda aka raba wa shugabannin jam'iyyar PDP domin yaƙin neman zaɓen Shugaba Jonathan a shekarar 2015, zaɓen da bai samu nasara ba.

Image caption Kudaden da aka gano a gidan Andrew Yakubu

Wasu bincike-binciken kuma sun bayyana yadda tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke tare da muƙarrabanta suka wawashe kuɗaɗen man fetur na ƙasar. Ban da wannan, gwamnatin Buhari ta gano wasu hanyoyin da ake sace kuɗaɗe, kamar ƙarin da ake yi wa kasafin kuɗi.

Amma mafi ban mamaki ga 'yan Nijeriya shi ne batun dalar Amurka miliyan 10 da hukumar EFCC ta gano, wadda tsohon shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, wato Andrew Yakubu ya ɓoye a unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna.

Akwai kuma maganar dalar Amurka miliyan 40 da shugaban hukumar tara bayanan sirri na ƙasa ya ɓoye a wani gida a Ikoyi.

Amma duk da waɗannan nasarori, wasu masana suna sukar yadda shugaba Buhari ke gudanar da yaƙi da cin hanci da rashawar. Suna cewa gyaran na buƙatar sabbin dabarun zamani ne, kafin a iya shawo kan lamarin.


Image caption Mahmud Jega manazarci ne kuma dan jarida a Najeriya

Shugaba Buhari da masu magana da yawunsa sun ɓata lokaci mai tsawo suna tura laifin halin da ƙasar ke ciki ga gwamnatin Shugaba Jonathan, wanda ba laifi ba ne. Amma gwamnatin ta riƙa yin tafiyar hawainiya, kuma kamar babu wani tsarin da take bi wajen magance al'amarin.


Tattalin arziki ya yi ƙasa

Fannin da Shugaba Buhari bai samu nasara sosai ba shi ne na haɓaka tattalin arziƙi. Koma-bayan tattalin arziƙin ya zo daidai lokacin da gwamnatin ta Buhari ta kama madafun iko.

Manyan batutuwa uku mafi muhimmanci su ne - faɗuwar farashin mai a kasuwar duniya, da gagarumar sata lokacin mulkin Jonathan, da dakatar da tayar da ƙayar baya a yankin Neja Delta, da kuma batun zagon ƙasa da ake yi wa masana'antun man fetur da hanyoyin samar da wutar lantarki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ayyukan masu tayar da kayar baya na yankin Naija Delta sun jawo tabarbarewar tattalin arziki

Shugaba Buhari da masu magana da yawunsa sun ɓata lokaci mai tsawo suna tura laifin halin da ƙasar ke ciki ga gwamnatin Shugaba Jonathan, wanda ba laifi ba ne. Amma gwamnatin ta riƙa yin tafiyar hawainiya, kuma kamar babu wani tsarin da take bi wajen magance al'amarin.

A halin yanzu, tattalin arziƙin ya fara farfaɗowa, saboda ƙaruwar farashin mai da kuma dakatar da rikicin 'yan Neja Delta.

Ina aka kwana kan alƙawurran da ya yi?

Ban da waɗannan fannonin, gwamnatin Buhari ta gaza samun nasarori da dama, musammam alkawurran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zabe. Game da samar da wutar lantarki, maimakon lamarin ya gyaru, sai ma ya kara taɓarɓarewa.

Buhari ya magance tsarin nan na sata ta hanyar biyan tallafin man fetur, shi ma sai da ya ƙara farashin litar mai daga Naira 97 zuwa Naira 145.

Alƙawuran tabbatar da jin dadin al'umma, kamar bai wa matasa 500,000 aikin koyarwa, da biyan talakawa Naira 30,000 a kowane wata da sama wa masu kananan masana'antu basuka masu saukin biya, duka ba su samu ba, ko kuma a ce ana tafiyar hawainiya wajen aiwatar da su.

Sai dai a iya cewa babban alƙawarin nan na ciyar da ɗalibai abinci a makarantun gwamnati sau ɗaya a yini da ba su madara duk an kasa fara su.

A wannan lokacin da muke duba irin rawar da gwamnatin Buhari ta taka cikin shekara biyu na farko, yawancin 'yan Nijeriya suna fatan shugaban ya samu cikakkiyar lafiya, domin ya dawo ya ci gaba da sauran aikin gyaran ƙasa na shekara biyun da suka rage.

Image caption Da yawan 'yan Najeriya na addu'ar Buhari ya samu lafiya ya karasa shekara biyunsa

Labarai masu alaka