Ya ya rayuwar 'ya'yan mashaya giya take?

Rayuwar 'ya'yan mashaya giya na shiga garari
Image caption Rayuwar 'ya'yan mashaya giya na shiga garari

Daya daga cikin yara biyar a Birtaniya sun ce, shaye-shayen da iyayensu ke yi ya haifar musu da matsala, kuma matsalar ta yi tasiri a lokacin da suka fara girma. Jo Morris ya tattauna da wasu mata inda suka bayyana masa yadda suka girma da iyayensu da suka kasance mashaya.

Daya daga cikin matan Karen, ta ce, "Wasu mutanen suna bayar da labari ne a kan littattafan da suka karanta, ko fina-finan da suka kalla, sai dai mu za mu bayar da labari ne na zahiri a kan yadda iyayenmu suka kasance mashaya."

Karen da kawarta Liz sun hadu ne a wurin aiki a lokacin suna da shekara 20, sun kuma shakuwa cikin kankanin lokaci da suka gane cewa labarinsu iri daya ne.

Liz ta ce, ba ko wacce magana za ka fada wa mutumin da bai san kanta ba."

Yaken da suke ya taimaka musu wajen jure tuna abubuwa marasa dadi da suka faru. Kamar lokacin da mahaifiyar Liz ta sayar da kayan wasanta don ta samu kudin da za ta sha giya. Ko lokacin da Baban Karen ya tafi mashaya maimakon ya daukota daga makaranta.

Karen ta yi dariya ta ce,"Abin ne kamar a fim".

Sun tuna lokacin da suke tafiya gida daga makaranta cikin tsoro.

Lokacin da Liz ta kai shekara takwas zuwa tara ne kawai ta gane cewa kawayenta ba irin wannan rayuwar suke yi ba.

Wata rana, mahaifiyarta ta karar da dukkan kudinta wajen sayen giya, a lokacin ba su da wani abu sai buhun dankalin turawa.

Liz ta yi dariya ta ce, mun kira wannan lokaci da "Makon dankalin turawa". Mun shafe mako guda muna sarrafa dankalin turawa ta hanyoyi daban-daban.

Hilary mai shekara 55, ta taso a cikin zuri'ar da suke da rufin asiri a kasar Sunderland, mahaifinta babban likita ne. Suna zaune cikin rufin asiri sai dai mahaifiyarta 'yar giya ce.

Ta ce, "Na tuna lokacin da nake makaranta, wata yarinya a ajinmu tana bude abincinta sai ta ce, 'Kai! Ba bota sosai a jikin biredina.' Sai kawai na ga ai ita kukan dadi ma take yi."

Ba wanda yake yi wa Hilary abin karin kumallo na zuwa makaranta. A takaice ma ita ce mai kula da kaninta har ya yi bacci, ta shirya shi zuwa makaranta, ta kuma tabbatar da ya ci abinci.

Da farko mahaifiyarta ta fara shan giyar ne da kofi daya 'idan tana girki', daga baya kuma ta koma shan kwalba daya a rana.

Hilary ta ce, "Ba za ka iya hira da ita ba saboda ko yaushe a buge take, tana nan amma kamar ba ta nan".

Mahaifiyar Liz mai son ado ce, amma bayan da ta fara shan giya da wuya ka gan ta da kwalliya a fuska, 'ta zama wata gata nan ne kawai,' in ji ta.

Liz ta fara rayuwarta ne ta rashin mafadi, sakamakon sakacin da aka yi da ita. Lokacin da ta kai shekara 15 ta shiga cikin gararin rayuwa, daga baya kuma ta dawo cikin hankalinta ta samu kula. Inda ta godewa kawayenta da suka taimaka mata a kan kubutar da ta yi.

Ta ce, "Na zama ta gari a lokacin da na hadu da kawaye nagari wadanda suka taimaka mini, wadanda ba sa shaye-shaye".

A lokacin da ta ga kawayenta suna karatu a jami'a ne, sai hakan ya ba ta sha'awa, ita ma ta shiga.

Labarai masu alaka