Akwai bukatar bai wa Kiristoci kariya a Gabas Ta Tsakiya — Trump

Archbishop Georg Ganswein sun gaisa da shugaba Trump Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Archbishop Georg Ganswein ya gaisa da shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wata takaitacciyar ganawar sirri da Fafaroma Francis a ci gaba da ziyarar da yake kai wa kasashen waje.

Fadar Fafaroman ta ce, bayan ganawar da suka yi ta "musayar ra'ayi" a kan batutuwan da suka shafi kasa-da-kasa da dama da ba a bayyana ba, sun tattauna a kan bukatar ci gaba da samun kyakkyawar alaka.

Har ila yau, Mista Trump ya gana da shugaban Italiya da kuma Firai ministan kasar.

Daga baya kuma zai daga zuwa Brussels don halattar taron Nato.

Da farko ya ci alwashin taimakawa Isra'ilawa da Falastinawa samun nasarar zaman lafiya, a yayin da yake kammala ziyarar tasa ta Gabas Ta Tsakiya.

Shugaban Amurkan ya fara ziyarar kasashen ne ta yini biyu da kasar Saudiyya a cikin karshen mako, inda ya yi kira ga kasashen Musulmai da su yi amfani da ikonsu wajen kawar da tsattsauran ra'ayi.

Mista Trump da tawagarsa sun sauka a fadar Fafaroma kafin karfe 8:30, a daidai lokacin da aka tsara ganawar.

Mutanen sun kebe inda suka tattauna ta tsawon minti 20.

Daga bisani ne fadar Fafaroma ta ce, ta yi alkawari a kan cewa, tana aiki tukuru don ganin an yi "Rayuwa da samun 'yancin bauta" tare da bayyana cewa tana fatan samun hadin kai wajen yi wa mutane aiki a bangaren da ya shafi lafiya, da ilimi, da kuma taimaka wa 'yan gudun hijira".

A kan mu'amalar kasa da kasa kuwa, sun tattauna kan yadda za a samu ingantaccen zaman lafiya a duniya ta hanyar sulhu a siyasance da addinance, sun kuma duba bukatar kare al'umar Kiristoci da ke Gabas ta Tsakiya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Trump da Pope sun yi musayar kyautuka

Labarai masu alaka