'Yan sanda sun kai samame gidan jagoran Shi'a a Bahrain

kungiyar agaji da duniya Hakkin mallakar hoto ADHRB
Image caption Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty ta ce an harbi daya daga cikin mamatan ne a kai

Mutane biyar ne suka mutu, bayan da 'yan sanda a Bahrain, kasar da ke karkashin mulkin Sunni, suka kai samame gidan wani fitaccen malamin 'yan Shi'a a kasar.

Ministan cikin gida ya ce an kama mutum 286, bayan da suka kai wa jami'an tsaro suka hari a kauyen Diraz.

Masu fafutuka sun ce jami'an tsaro sun bude wuta kan mabiya malamin Sheikh Isa Qassim, wanda ba a tsare yake hannun hukuma ba.

Lamarin dai ya zo kwanaki biyu bayan an zargi malamin da laifukan da suka shafi cin hanci.

An dai yanke wa Sheikh Qassim hukuncin shekara daya a gidan kaso, tare da cin tararsa dinari 100,000 kwatankwacin dalar Amurka 265,000, bayan da aka same shi da laifin halatta kudaden haram.

A watan Yunin da ya gabata ne, kasar Bahrain ta kwace masa takardar izinin zama dan kasar, inda ta zarge shi da yin amfani da mukaminsa wajen tayar da hargitsi.

A wata sanarwa da ministan cikin gidan kasar ya fitar ranar Talata, ya ce an kai samamen ne "saboda kare lafiyar jama'a".

"Lokacin arangmar, 'yan tawayen dauke da makamai sun far wa jami'an 'yan sanda inda suka dinga jifan su da wukake da adduna, al'amarin da ya janyo 'yan sandan suka mayar da martani su ma," a cewar sa.

A wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan ta fitar ta ce, Jami'an 'yan sanda 19 ne suka samu raunuka a arangamar, kuma an tabbatar da mutuwar mutum biyar,

Shaidu sun ce 'yan sanda sun yi ta harba harsasan roba da hayaki mai sa kwalla, ga masu zanga-zangar da ke jefa duwatsu kan jami'an.

Labarai masu alaka