Ɗan Nigeria ya samu kyautar naira miliyan 12 a Birtaniya

Godwin Hakkin mallakar hoto Royal Academy of Engineering
Image caption Godwin ya fara tunanin kafa shafin Tuteria ne yayin da yake koyar da darasin lissafi.

Wani malamin lissafi ɗan Najeriya, Godwin Benson, ya samu kyautar Dala dubu 32 (kimanin Naira miliyan 12) daga Kungiyar Injiniyoyi ta Birtaniya wato UK Royal Academy of Engineering.

An ba shi kyautar ne saboda wani shafin intanet da ya ƙirƙiro mai suna Tuteria, wanda yake taimakawa iyaye wajen samarwa 'ya'yansu malamai da za su rika koyar da su darussa a gida.

Har ila yau, ya ce fara tunanin kafa shafin ne yayin da yake koyar da darasin lissafi.

"A lokacin mun yi yarjejeniya da mahaifin wani dalibina kan zai rika biyana dubu shida a ko wnane wata idan na koyar da ɗansa, amma sai ya ki biyana," in ji Godwin.

Ya ce daga baya ne sai ya fahimci cewa mutumin ya kwashe watanni yana neman malamin da zai rika koyar da dansa a gida, ba tare sanin cewa Mista Godwin yana kusa da unguwar da yake ba.

Duk da cewa sun samu matsala da mutumin, daga nan ne a shekarar 2015 Godwin ya fara tunanin buɗe shafin Intanet da zai rika sada iyayen yara da malamai masu koyar da yara darussa a gida.

Ya ce masu bukatar malaman za su iya bayyana hakan ne ta intanet kuma su biya wani abu don bai wa malaman kwarin gwiwar fara aikin.

Shugaban Kungiyar Injiniyoyin Malcolm Brinded, ya ce shafin Intanet din Godwin ya sauya yadda 'yan Najeriya suke samun ilimi.

Labarai masu alaka