Za ki yarda mijinki ya yi tafiyar shekaru ya bar ki?

Samira Razak ta ce auren nesa ba shi da amfani amma soyayya ta ci karfinta
Image caption Samira Razak ta ce auren nesa ba shi da amfani amma soyayya ta ci karfinta

Me ke sa mazan Ghana ke yin balaguro zuwa kasashen waje inda suke kwashe shekara da shekaru ba tare da sun koma wurin matansu ba? Wacce illa hakan ka iya yi? Wanne mataki ya kamata a dauka domin shawo kan wannan matsala?

Aure al'amari ne da ya shafi shakuwa da juna da kauna da hakuri da debe wa juna kewa.

Haka kuma aure, abu ne da ke bukatar masu yinsa su zauna tare domin lura da juna da kuma bai wa juna shawarwari.

Bahaushe yakan ce garin masoyi ba shi da nisa saboda ya nuna irin dangantaka ta kut-da-kut tsakanin masoya, ta yadda za su iya yin komai domin su farantawa juna rai.

Sai dai a kasar Ghana akwai wani nau'in aure da masana ke ganin bai cika wannan sharuda ba.

Wannan aure kuwa shi ne auren boga: wato auren mutumin da yake zaune a kasashen waje, musamman Amurka da Turai.

Mazan kan auri matan ne, ko dai kafin su tafi kasashen na waje, ko kuma bayan sun aure su.

Babban abin lura a cikin irin wannan aure shi ne mazan kan tafi kasashen waje inda za su kwashe shekara da shekaru basu koma gida ba.

Binciken da na yi ya nuna cewa yawancin mazan da ke tafiya kasashen na waje, mutane ne da ba su da izinin zama a can don haka ba za su iya kai iyalinsu ba saboda su kan su wasan-buya suke yi da hukumomin kasashen don tsoron kada a kama su a tasa keyarsu zuwa gida ko kuma a daure su.

Image caption "Tarbiyantar da 'ya'ya ba tare da maigida ba na da wahala," in ji Aisha Umar

'Zaman larura'

Yawancin matan da na tattauna da su a Ghana, sun bayyana mini cewa sun hadu da mazan ne a kasar amma daga bisani suka yi balaguro zuwa kasashen waje kuma daga can ne za su aiko a daura musu aure.

Samira Razak, wata matar aure ce da suka yi aure da mijinta bayan shekara uku yana neman ta, ta shaida min cewa shekarar ta hudu ba ta sanya shi a idonta ba.

"Mijina ya tafi Canada tun ma kafin mu yi aure. Daga can ne ya aiko aka daura mana aure amma har yanzu ban gan shi ba. A wajen mahaifiyarsa nake zaune, kuma ita ce ke ba ni umarni a kan duk abin da zan yi. Shi kuma yana kira na a kai-akai. Yana aiko min da dala 100 duk wata domin na biya bukatun da ke gabana", in ji ta.

Samira Razak ta ce rashin sanya mai gidanta a idanunta yana sosa mata rai amma tana ci gaba da hakuri "saboda matukar kaunar da nake yi masa. Na san cewa wataran zai dawo Ghana".

A nata bangaren, Aisha Umar, ta ce mijinta ya tafi balaguro kasashen waje ne bayan sun haifi 'ya'ya uku kuma tana da cikin da na hudu.

A cewarta, "Mai gidana ya tafi Brazil ne mako biyu kafin na haifi 'yata ta hudu amma har yanzu bai dawo ba. Ya shekara biyar ba mu gan shi ba. Amma yana aiko mana da kudi".

Ta kara da cewa kudin da yake aiko musu ba ya isarsu, musamman ganin cewa yaran na bukatar zuwa makaranta.

Aisha Umar ta ce, "Ni ce nake yin sana'a domin na ciyar da 'ya'yana kuma wallahi rayuwar da muke yi na da matukar wahala. Kusan kullum sai 'ya'yana sun tambaye ni yaushe mahaifinsu zai dawo. Zan so ya dawo kusa da ni amma ya ce aikin da suke yi na bukatar lokaci sosai kuma ba shi da takardu don haka idan ya dawo gida mai yiwuwa ba za a bar shi ya sake shi kasar ba. Yanzu dai muna yin zaman larura".

Sai dai mazajen sun bayyana suna tafiya suna barin matansu ne saboda neman abinci kuma babu yadda za su iya ne shi ya sa suka bar su.

Sali Adams-Abba ya shaida wa BBC cewa, "Na tafi birnin Hamburg na kasar Jamus inda na yi shekara bakwai ban dawo ba. Amma na koma gida a shekarar da ta wuce na yi wata uku. Yanzu na koma Jamus shekara daya kenan. Ina kewar iyalina kuma idan a sona ne zan zauna tare da su amma hakan ba zai yiwu ba saboda yanayin rayuwa."

Image caption Wasila Adams ta ce ta ce mijinta ya kwashe shekara bakwai bai koma gida ba

'Yi wa tufka hanci'

Da alama yawan tafiyar da mazan kan yi su kwashe shekara da shekaru ba su koma gida ba na ci wa Malamai, wadanda su ne ke daura irin wannan aure, tuwo a kwarya.

Rahotanni sun ambato babban limamin masallacin Accra Sheikh Usman Nuhu Sharubutu na cewa daga yanzu ba za a sake aura auren duk mutumin da zai bar iyalinsa ya yi tafiyarsa kasashen waje ba.

Wani Malami, Sheikh Adam Alfarisi, ya shaida min cewa a Musulunce bai kamata miji ya tafi ya bar matarsa tsawon shekaru ba.

A cewarsa, "Ya kamata a raba irin wannan aure domin mijin ya shiga hakkin matarsa. A Musulunce ba a yarda miji ya yi tafiyar shekara da shekaru ba tare da iyalinsa ba".

Image caption Hajiya Zuwaira Idris: "Na daina makaranta domin mu yi aure amma ya tafi ya bar ni"

Masu sharhi na gani matakin da Malamai za su dauka ka iya rage wannan matsala idan har masu yin irin wannan aure ba su sauya dabara ba, tunda dai Hausawa na cewa ma so abinka ya fi ka dabara.