Ba a yi yunkurin juyin mulki a Nigeria ba — Buratai

Buratai ya ce 'yan Najeriya su daina yarda da wannan jita-jitar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Buratai ya ce 'yan Najeriya su daina yarda da wannan jita-jitar

Hukumomin sojin Najeriya sun yi kira ga 'yan kasar da su watsar da rahotannin da ake yadawa na jita-jitar yiwuwar juyin mulki.

Shalkwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda take sukar jita-jitar da wasu ke bazawa na yiwuwar juyin mulki a kasar.

Akwai alamar cewa sauyin aikin da babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya yi wa manyan hafsoshin sojin kasar, ya biyo bayan wadannan bayanan na yiwuwar juyin mulki ne.

A sanarwar da kakakin shalkwatar tsaro ta sojojin Najeriya, Manjo-Janar John Enenche, ya fitar, ya tabbatar da cewa babu wani dalilin da zai sa 'yan Najeriya su damu, yana cewa sojojin kasar suna bai wa mulkin dimokradiyya cikakken goyon baya a kasar.

Ya kara da cewa bayanan babban hafsan sojojin kasar game da dangantakar da ke tsakanin wasu fararen hula da sojoji abu ne da aka saba yi domin jan kunnen sojojin, kuma domin su tabbata ba su kauce wa tsarin aikinsu ba.

Akwai alamun shugaban sojojin na mayar da martani ne, game da wasu rahotanni daga wasu sassa da ke cewa akwai yiwuwar juyin mulki.

Manyan 'ya siyasa da masu kare radin dimokradiya sun yi kiraye-kiraye da a gabatar da bincike bayan da aka sami wasu rahotanni cewa wasu jami'an soji za su hambarar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, a lokacin da yake hutun neman lafiya a Birtaniya.

Ita ma a nata bangaren fadar gwamnatin kasar, ta bakin mai magana da yawun shugaba Buhari, Mr Femi Adesina, ya yi kira ga 'yan kasar da kar su yarda da wannan rade-radi don ba gaskiya ba ne.

Labarai masu alaka