Nigeria: Za mu mayar da Kano ƙasaitaccen birni - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin ciyar da jihar Kano gaba

A Najeriya, gwamnatin jihar Kano da ke arewacin kasar ta cimma yarjejeniya da wasu kamfanonin kasashen waje dana cikin gida da nufin zuba jari wajen samar da ababen more rayuwa a jihar.

An dai cimma yarjejeniyar da akalla kamfanoni guda goma wadanda suka fi karkaka ga harkar inganta sufuri da samar da makamashi.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce "mun ce muna son mayar da birnin Kano kasaitacce birnin wanda za'a kwatanta shi da sauran birane na duniya, kuma wannan yana bukatar abubuwa da yawa, saboda haka muka kira masu sa hannun jari kamfanoni guda goma wasu ma har sun fara"- in ji shi.

Jari mafi kauri ya fito ne daga hannun kamfanin Eighteen Engineering Company na kasar China, wanda ya cimma yarjejeniyar gina hanyar jirgin kasa na zamani a cikin birnin Kano da kewaye.

An dai ƙiyasta cewa aikin gina hanyar jirgin kasa na zamani zai lakume dala biliyan daya da miliyan dari takwas.

Kamfanin Dangote na daga cikin kamfanoni na cikin gida dake shirin zuba jari a jihar.

Direktan Kamfanin Dangote a jihar Kano Alhaji Mansur Ahmed ya ce "Kamfanin Dangote zai sa jari wajen bunkasa masana'atu da kuma bangaren samar da makamashi da hasken rana inda zai kashe dala miliya 150 kuma za'a kammala aikin cikin shekaru biyu,"- in ji shi.

Jihar Kano dai ita ce cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya.