"Yadda 'rashin ingancin' ilimin Nigeria ke sa mu tafiya waje"

BUK Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dumbin 'yan Najeriya ke barin kasarsu don zuwa Ghana karatu

Matsalolin da suka addabi Najeriya, kama daga rashin ingantattun asibitoci zuwa rashin kwararrun Malaman makaranta, na cikin abubuwan da ke tilastawa 'yan kasar fita kasashen waje domin neman biyan bukatunsu.

Tun ma lokacin hankali na kwance, 'yan Najeriya kan fita kasashe irin su Amurka da Burtaniya domin neman ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.

Daga bisani kuma, lokacin da al'amura suka tabarbare 'yan kasar sun mayar da hankalinsu zuwa kasashen Larabawa da nahiyar Asia domin neman lafiya da ilimi.

Yanzu ba wani abin mamaki ba ne idan aka ji dan Najeriya ya tafi kasashen Indiya ko Hadaddiyar Daular Larabawa, musamman ma birnin Dubai domin neman lafiya.

Haka kuma 'yan kasar ta Najeriya kan fita zuwa Malaysia da Singapore domin neman "ingantaccen" ilimi.

A Afirka kuwa, 'yan Najeriya sun mamaye Jami'o'i a kasashen Uganda da kuma Ghana.

Na leka Jami'o'i da dama a nan kasar Ghana inda na ga daruruwan 'yan Najeriya da ke karatu a fanni daban-daban.

Hakkin mallakar hoto Halima Umar
Image caption Nasidi Adamu Yahaya na tattaunawa da wasu dalibai

'Ba mu da mafita'

Akasarin 'yan Najeriyar da na tattauna da su sun ce sun shigo wannan kasa domin yin karatu ne saboda al'amarin karatun Najeriya ya tabarbare.

Nuhu Mustapha Hunkuyi, wani dalibi ne a wata Jami'a mai zaman kanta, kuma ya shaida min cewa Jami'o'in Najeriya sun ki ba shi gurbin karatu duk da yake ya cika dukkan sharudan samun gurbin.

"Na rubuta jarrabawar SSCE kuma na yi nasara a dukkan darussan da na rubuta amma duk Jami'ar da na tuntuba babu wacce ta amince ta ba ni gurbin yin karatun Digiri, sai kawai na yi tahowa ta nan Ghana," in ji shi.

Ya kara da cewa zuwansa Ghana ya zamar masa gobarar titi a Jos "domin kuwa karatun da nake samu a nan ya fi na Najeriya inganci".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daliban sun ce a Ghana an fi koyar da karatu a aikace ba a baki kawai ba kamar NAjeriya

Shi kuwa Ismail Abari ya gaya min cewa ya zo kasar Ghana ne saboda babban makasudin da ya sa shi da mahaifansa suka yanke shawarar zuwansa kasar Ghana karatu shi ne rashin samun ilimi mai inganci a Najeriya.

"Ya kamata ka sani cewa a Najeriya an fi koyar da karatu a baki; su kuwa kasar Ghana suna koya wa mutum karatu ne a aikace. Ka ga kuwa ba za a hada abin da za a yi maka da baki da wanda za a koya maka a aikace ba," in ji Ismail Abari.

Ina mafita?

Ya kara da cewa Najeriya ta yi kaurin suna wajen yajin aikin Jami'o'i, lamarin da kan sanya "dalibin da ya kamata ya yi shekara hudu a Jami'a zai yi shekara da shekaru bai kammala jami'a ba. Amma ba mu taba fuskantar yajin aiki a nan ba."

Wani Malamin Jami'ar Legon da bai so a fadi sunansa ba, ya shaida min cewa ingancin ilimin kasarsu ya fi na Najeriya ne saboda muhimmancin da gwamnati ke bai wa fannin ilimi, ko da yake ya kara da cewa su ma suna fuskantar matsalolin da ba a rasa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan yin yajin aiki a jami'o'in Najeriya in ji daliban

Hukumomin Najeriya dai sun sha cewa suna kokarin magance matsalolin da suka addabi harkar ilimi, wadanda ke sa wa 'yan kasar ke fita kasashen waje neman ilimi.

Sai dai sun ce tabarbarewar ilimi ya soma ne tuntuni saboda kawar da kai daga gwamnatocin baya.

Masana dai na ganin har yanzu gwamnatin kasar ba da gaske take ba a shirinta na farfado da ilimi saboda har yanzu kasafin kudin da ake ware wa fannin bai kai mizanin da hukumar kula da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka