Tsananin addu'a ba zai sauya Nigeria ba sai an yi aiki tuƙuru — Osinbajo

Osinbajo Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Yemi Osinbajo na kokarin karfafa wa ma'aikatan kasar gwiwa ne

Muƙaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce duk yawan addu'a da azumin da mutane za su yi, ƙasar ba za ta ci gaba ba in har wasu daga cikin al'ummar ba su yi aiki tuƙuru irin wanda zai sa ƙasar ta samu abin da take so ba.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da ma'aikatan gwamnati ranar Laraba a Abuja, kan rattaba hannun da ya yi a baya-bayan nan kan muhimman dokoki uku, wadanda za su saukaka yin kasuwanci a kasar.

Mista Osinbajo ya kuma yi kira ga ma'aikatan gwamnati da su sake zage dantse wajen kyautata wa kasarsu don ci gabanta.

Ya ce "Na lura mutane kan yi shewa ne kawai idan suka ji an yi maganar karin albashi. To bari na baku tabbaci cewa ba ku da matsala, saboda da ni da shugaban kasa duk ma'aikatan gwamnati ne kuma mun san ciwonku".

Ya kara da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha cewa ba shi da wani aiki da ya wuce bautawa kasarsa.

Mukaddashin shugaban kasar ya ce duk kasar da a ka ga ta ci gaba, ta kuma bunkasa tattalin arzikinta to mutane ne suka yi aiki tukuru ba zallar addu'a ba.

"Na tabbata mutane da yawa sun san cewa ni Fasto ne, wanda ya yarda da addu'a, na kuma san amfanin abin da ka shuka shi za ka girba, al'amari ne da addu'a kan yi tasiri amma idan an hada ta da aiki tukuru."

Hakkin mallakar hoto Twitter

Ya kuma jaddada bukatar cewa 'yan Najeriya su shiga harkar noma ka'in-da-na'in, musamman ma ta bangaren noman shinkafa don a samu wadatar abinci a kasar.

Ya kara da cewa, "A makon da ya gabata na gana da manyan sakatarorin ma'aikatun gwamnatin inda muka tattauna kan batun rashin aikin yi. Babban jarin da za mu zuba a rayuwarmu shi ne a bangaren ilimin 'ya'yanmu.

Muna yin bakin kokarinmu don ganin mun tura su jami'o'i a kasashen waje, wasu lokutan ma har makarantun sakandare a waje suke yi, amma idan sun kammala sai su kasa samun aiki. Ba abu mafi ciwo irin ka ga 'ya'yanka sun kammala makaranta amma ba aikin yi".

Ya ce ya shafe shekaru yana duba wannan matsala sosai. "Ya ya za mu kirkiri ayyuka? Ta ya ya za mu samarwa miliyoyin matasa aiki a yau da gobe?"

Sai dai wannan magana tasa ta janyo muhara mai zafi da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumuntar kasar, inda wasu suka dinga mayar da martani mai zafi, yayin da wasu kuma suke ganin batun nasa daidai ne.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Wasu daga cikin martanin da 'yan Najeriya suka yi a Twitter

Wasu daga cikin martanin da aka mayar na cewa, "Matsalolin Najeriya ba na addini ba ne, matsaloli ne da ya kamata dan adam ya gyara a kan kansa, muna bukatar mayar da yawancin coci-coci kamfanoni don mu inganta tattalin arzikinmu."

Wani kuwa cewa ya yi, "Aiki tukuru ba tare da addu'a ba zai sa mu zama kamar masu bautar gumaka." Inda wani ya mayar da martani cewa, "Ai kuwa tsananin addu'ar ba tare da aiki tukurun ba shi ne ya sa muka samu kanmu a wannan yanayin da muke ciki."

Shi kuwa wani cewa ya yi, "Muna son aiki tukurun ya fara da haramtawa jami'an gwamnati tafiya kasashen waje don zuwa asibiti...."

Wasu kuwa cewa suka yi, "Aiki tukuru? Bayan shugabanka yana can London ba aikin da yake yi. Ai ya yi murabus kawai don a samu a yi aiki tukurun."

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government

Labarai masu alaka