Kun san matan da al-Shabab 'ta mayar bayi'?

Wasu matan da suka kubuta daga kungiyar al-Shabab
Image caption Wasu matan da suka kubuta daga kungiyar al-Shabab

A lokacin da Salama Ali ta fara bincike kan wasu 'yan uwanta biyu da suka bata, a shekarar da ta gabata, ta gano wani al'amari mai ban tsoro - ba matasan Kenya masu tsattsauran ra'ayi ne kawai ke shiga kungiyar al-shabab ba, ta gano kungiyar na sace mata kuma tayi safararsu zuwa makwabciyar kasar Somaliya, inda ake mayar da su bayi domin a yi lalata da su.

Dole Salama ta gudanar da binciken neman 'yan uwan nata cikin sirri, saboda duk wata alama dake nuna tana da alaka da kungiyar al-Shabab mai biyayya ga al-Qaeda na iya janyo tuhuma daga hukumomin tsaron kasar.

Sai ta rika ganawa da wasu mata, a cikin sirri a birnin Mombasa, domin neman bayanai ne game da 'yan uwansu maza da suka bata.

Salama ta ce, "Mun fahimci cewar muna da yawa".

Amma Salama ta gano wani batu na daban - labarin wasu mata da aka kaisu Somaliya ba da san ransu ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari bayanin matan da al-Shabab suka mayar bayi

Matan sun hada da matasa da kuma tsofaffi, Musulmai da kuma Kirista, daga yankin Mombosa, har da wasu daga yankunan gabar tekun Kenya. Akan yi masu alkawarin samar masu ayyuka masu albashi mai tsoka a birane ko a wasu kasashe, daga nan sai a yi garkuwa da su.

A watan Satumbar da ya gabata Salama ta samu horona musamman, kuma ta kafa wata kungiya ta sirri don taimaka ma irin wadannan matan. Matan da suka samu labarin kungiyar sun rika nemanta domin su shiga kungiyar.

Ta ce, wasu sun zo da jarirai, wasu da cutar kanjamau, wasu ma da tabin hankali, wanda hakan sakamakon matsalolin da suka fuskanta ne.

Na gana da wadannan matan masu karfin hali, a cikin wani daki mai duhu, wanda suka ba ni labarin da ba a taba jin irinsa ba.

Daya daga cikin matan ta ce, "A lokacin, maza na zuwa domin su yi lalata da ni, ba zan iya fada miki adadinsu ba".

"A shekarun nan uku kowa ne namiji na zuwa ya yi lalata da ni", ta rika girgiza kanta sabili da tuna halin da ta shiga.

Wata matar kuma cewa ta yi,"Su kan kawo maza biyu ko uku ne suyi lalata da kowace mace a kowane dare. An yi mana fyade ba adadi".

Wasu matan an tilasta masu zama "matan" 'yan kungiyar al-Shabab, wasu kuma an mayar da su karuwai ne a wani gida.

Image caption Wasu matan da suka kubuta daga kungiyar al-Shabab

Kungiyar al-Shabab na neman kafa daular Islama ne a Somaliya, suna kai hare-hare har cikin makwabtan kasashe, kuma an tura sojojin Kawancen Afirka don su yake su.

Wata sabuwar mamba a kungiyar Salama mai suna Faith kwananan ta tsere daga kungiyar.

Tana 'yar shekara 16 ne wasu tsofaffin ma'aurata suka ce mata sun dauke ta aiki a Malindi. Saboda tana matukar neman aikin yi, kashe gari sai ta shiga wata mota tare da wasu fasinjoji 14 kuma an ba su ruwa mai bugarwa suka sha ba da saninsu ba.

Faith ta ce, "A lokacin da muka dawo hayyacinmu, akwai wasu maza guda biyu a cikin dakin. Sun rufe mana fuskokinmu da bakaken kyalle kuma sun yi mana fyade a dakin".

An kara ba Faith ruwa mai bugarwa, daga baya sai ta ganta a cikin wani kungurmin daji, inda aka shaida mata cewa idan ta yi yunkurin tserewa za a kashe ta.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dajin da 'yan Al-Shabab suke boye mata su mayar da su bayi

Ta samu ciki sakamakon fyaden da aka yi mata, kuma ta haifi danta a dajin ita kadai.

Ta ce, "Kakata unguwarzoma ce, saboda haka na san yadda ake wasu abubuwan, ni kadai na yi komai a dajin, ni kadai na fitar da wannan jaririyar."

Daga karshe Faith ta samu kubuta da 'yarta, bayan da wani mai maganin gargajiya wanda ya shiga dajin domin neman sauyoyi ya gamu da ita. Ya kuma nuna mata hanyar da zata fita daga dajin. 'Yarta tsirara ta rayu a cikin dajin, kuma yanzu rayuwar cikin gari na mata wahala, kuma ba ta iya yin barci da daddare har sai an fita da ita waje kuma sai tana hannun mahaifiyarta.

Faith ta ce 'yarta ta saba da "rayuwa tamkar ta dabbobi a dajin".

Wasu matan da suka tattauna da BBC sun haihu a wurin da aka tsaresu.

Matar wani tsohon dan kungiyar al-Shabab mai suna Sarah ta ce wannan an tsara ne da gangan, domin samar da 'yan kungiyar da zasu gaji wadannan. Abu ne mai wuya mutane su iya rayuwa a sansanoni a Somaliya, amma abu ne mai sauki a canza tunanin yara.

Image caption Faith da 'yarta

Sarah ta ce, "A sansanin da aka tsare ni, akwai wasu matan da ake tura su domin su nemo matan da za su shiga kungiyar. Suna son matan domin su rika haihuwa ne".

Ta ce, yawancin mata 300 da suke sansanin 'yan Kenya ne.

Har ila yau, Salama na taimaka wa wadanda suka rasa 'yan uwansu, kamar Elizabeth, wacce ta yi wa 'yar uwarta ganin karshe shekaru biyu da suka gabata bayan da aka yaudare ta da wani aiki a Saudiyya.

Elizabeth ta ce, "Ta shaida mana cewa tana cikin hadari a Somaliya, a sansanin al-Shabab". Layinta ya daina aiki, kuma tun daga wancan lokacin ba ta kara ji daga 'yar uwarta ta ba.

Gwamnatin Kenya ta yarda cewa akwai matasala, amma kwamishinan yankin Mombasa Evans Achoki, ya ce, abu ne mai wahala a gano gaskiyar al'amarin, saboda matan ba su kai kukansu ba wajen hukuma ba.

Duk da cewa akwai wani shirin afuwa ga mayakan da suke dawowa daga Somaliya, amma ana samun rahotannin cewa wasunsu na bacewa, wasu kuma ana harbesu har lahira.

"Ana kallon duk wadanda suka tafi can da son ransu, ko ba da san ransu ba a matsayin masu laifi."

Mun boye sunayen matan dake cikin labarin saboda kare lafiyarsu.

Labarai masu alaka