An kama tattabara ɗauke da miyagun ƙwayoyi

An yi amanna cewa kwayoyin wadanda doka ta haramta yin ta'ammali da su ne Hakkin mallakar hoto AL-RAI
Image caption An yi amanna cewa kwayoyin wadanda doka ta haramta yin ta'ammali da su ne

Jaridar al-Rai ta kasar Kuwait ta bayar da rahoton cewa, Jami'an kwastam na kasar sun kama wata tattabara mai dauke da mugayen ƙwayoyi a bayanta.

Jaridar ta kara da cewa, an samu ƙwayoyi da suka kai 178 a cikin wani dan aljihu da aka manna a bayanta.

An kama tsuntsuwar ne a kusa da wani ginin kwastam da ke Abdali, kusa da kan iyakar Iraki.

Abdullah Fahmi ya shaidawa BBC cewa, jami'an kwastam sun dade da sanin cewa ana amfani da tattabaru wajen yin fasa-kwaurin kwayoyi, amma wannan ne karo na farko da suka kama tsuntsuwa a hukumance.

Hakkin mallakar hoto Al-RAI
Image caption Ana amfani da tattabara wajen aika sako

A shekarar 2015 ma, masu gadin wani kurkuku a Costa Rica sun kama tattabara dauke da hodar iblis da tabar wiwi a cikin wata 'yar jaka da aka manna mata.

A shekarar 2011 ma, 'yan sandan Kolambiya sun gano wata tattabara da ta kasa tashi wajen tsallake wani kurkuku mai tsayin gini, saboda nauyin da ya yi mata yawa na hodar iblis da nau'o'in tabar wiwi.

Tun zamanin Romawa ake amfani da tattabaru wajen aika sako.

Tattabaru na iya komawa gidajensu daga nisan tafiyar daruruwan kilo mita.

Labarai masu alaka