Me 'yan Niger Delta ke so daga wajen Buhari?

Naija Delta Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yanzu dai za a iya cewa an fara samun zaman lafiya da gudanar ayyukan hakar mai a yankin Naija Delta na Najeriya, bayan artabun da aka yi fama da shi na hare-hare kan wuraren hakar mai da bututan man, wadanda kungiyar masu gwagwarmaya da makamai ta Niger Delta Avengers ta rika daukar alhakin kaiwa.

Hakan kuwa ya kai ga raguwar adadin man da ake hakowa a yankin, kuma ya kara dulmuya kasar cikin matsalar koma bayan tattalin arziki.

Wannan kuwa ya biyo bayan yadda gwamnatin kasar ta fara aiki da wasu shawarwari ne, tun da ta shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki na yankin, da kuma mayar da wuka kube da masu gwagwarmaya da makamai na yankin suka yi.

Sai dai kuma, duk da haka, ana ganin wannan zaman lafiya da aka fara samu a yankin na Naija Delta, tamkar na wucin gadi ne. Saboda haka, akwai bukatar bin matakan da za su kai shi ga dorewa.

Prince Maikpobi Okareme, wani tsohon sakataren kungiyar sarakunan gargagjiya na yankunan da ke da albarkatun man fetur na Najeriya, kuma jagoran kungiyar garuruwa masu albarkatun man fetur da gas a Najeriya, ya shaida wa wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed cewa har yanzu da sauran aiki.

''Za a iya cimma nasarar tabbatar da zaman lafiya na dindin ne a zahirin gaskiya, idan muna da tsari na daidaito da gaskiya da adalci. Saboda yadda ake gudanar da abubuwa bai bayar da damar wanzar da adalci a gare mu ba''.

Prince Maikpobi Okareme yana ganin daya daga cikin muhimman abubuwan da har yanzu suke jin za a yi a kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin Naija Delta, shi ne sake fasalta kasar.

''Idan aka yi hakan ne, bangarori daban-daban da suka yi Najeriya, za su sami cikakken hakkin da ya dace da su, kuma su kasance suna rike da wuka da nama na albarkatun da ke yankunansu''.

Shi kuwa Kwamred Thomas Pepple, wani matashi mai fafutukar kare muhalli a yankin na Naija Delta, a hirarsu da wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed, ya yi tsokaci ne cewa ba yadda za a wanzar da zaman lafiya mai dorewa da barazana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu masu sharhi sun ce sai an kawar da sojoji daga yankin in ana bukatar zaman lafiya

''Idan ana maganar wanzar da zaman lafiya (mai dorewa), to a kawar da sojojin da aka jibge a yankin na Naija Delta. Ba fa za a iya yin amfanin da makami a ce za a tabbatar da gudanar zaman lafiya ba. Duk wani zaman lafiya da za a samu ta hanyar yin amfani da tsoratarwa, to ba tabbatace ba ne. Kuma a karshe sai ka ga matsalar da ake gudu ta sake dawowa''.

Mai fafutukar kare muhallin, ya ce a duk wani shirin wanzar da zaman lafiya mai dorewa, da kuma kokarin bunkasa yankin na Naija Delta, da za a yi, dole sai an hada da kowanne bangare na mutanen yankin.

''A yi tsayuwar daka wajen sanya ainihin mutanen yankin a ciki. Su shugabanni a iya tattaunawa da su a nasu matakin, amma a sanya matasa cikin lamarin. A kuma hada da masu fafutukar kare hakkin bil'Adama da muhalli, da kungiyoyin farar hula da dai sauran masu ruwa da tsaki.

"Kuma a gano irin matsalolin da ke addabar talakawan yankin, ta fuskar noma da ilimi da dai sauransu, a dau mataki kyauatata masu."

Akwai kuma bukatar duba batun cin hanci da rashawa game da kudaden da ake ware wa sha'anin bunkasa yankin na Naija Delta.

Domin Kwamred Pepple Thomas ya yi zargi cewa, ''Kudaden da ake ware wa yankin Naija Delta za ka tarar ko dai an sace su, ko an yi almundahanar su, ko kuma an yi amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba''.

An dade ana yin irin wannan zargi, amma kuma galibi wadanda abin ya shafa suna musanta hakan.

A yanzu dai an yi ittifaki, cewa ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta bi shawarwarin da suka dace, don ganin an ririta zaman lafiyan da aka fara samu a yankin Naija Delta, kuma a tabbatar da dorewarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yankin Naija Delta na da arzikin man fetur

Labarai masu alaka