Za a rika narkar da gawa a maimakon binnewa

Image caption An fara amfani da injin narkar da gawa shekaru biyar da suka gabata

A shekaru da dama mutane na amfani da hanyoyi biyu wajen jaza'izar mamatansu, wato binnewa da kuma konawa.

To sai dai wannan al'ada na nema zamewa tarihi a wasu sassa na kasar Amurka da Canada, domin kuwa sun gano wata hanya da za a rika narkar da gawar ta amfani da wani sinadari.

Kuma ana dab da fara wannan sabuwar al'ada a Burtaniya.

Sunan sinadarin "Alkaline Hydrolysis", amma ana cinikayyarsa da sunan "green cremation".

Masu wannan sabuwar fasaha sun ce, idan za mu binne gawa mukan bukaci abubuwa masu tarin yawa, misali katako wajen yin akwatin gawa, da likkafanin da za a sanya wa gawar, da kuma duwatsu ko itatuwa da za a rufe kabarin da su.

A kasar Amurka a kan yi wa kaburbura siminti, ko kuma a sanya akwatin cikin wani wuri na musamman wanda gawar ba za ta lalace ba.

Har ila yau, shi ma kona gawa na da nasa matsalar in ji sabuwar fasahar, domin kuwa yakan jawo dumamar yanayi, domin kuwa a yayin kona gawa daya kawai, injin kona gawar kan zafafa gidan ko makabartar har na tsawon mako daya, koda kuwa a yankin Minnesota mai tsananin sanyi ne.

Bradshaw daya ne daga cikin gidajen jana'iza 14 a duniya dake amfani da wannan sabuwar fasaha na "narkar da gawa". Kamar yadda suka bayyana sinadarin "Alkaline Hydrolysis" da ake amfani da shi, ba kawo wata matsala ga muhalli.

Suna amfani da farashi na bai daya, wato da manya da yara duk kudin daya ne, kuma sun ce wannan sabuwar fasaha na taimakawa wajen rage dumamar yanayi.

Ga abokan huldarsu da suka zabi da kar a binnesu- sukan samun rangwamen rabin kashi 80 cikin 100 na sinadarin.

To sai dai ba dumamar yanayi ne kadai dalilinsu, na bullo da wannan sabuwar hanyar ba.

Injin narkar da gawar wanda yakan lamushe kudi kimanain dala 750,000, za a girke shi ne a cikin cibiyar, kuma an fara aiki da shi shekaru biyar da suka gabata.

Jason Bradshaw, shi ne manajan cibiyar ya kuma ce, "mun so mu yi aikin cikin farashi mai sauki.

Muna jin dadin cewa mu ne na farko a wannan fannin - kuma mu ne na farko a kasarmu muna bukatar kara bunkasa wannan kasuwanci namu".

Jason, wanda ke da digiri a fannonin Ilimin halittu (Biology), da ilimin sinadarai (Chemistry), ya bayyana cewa injin na auna nayin kowacce gawa sanna ya lissafa yawan ruwa da sinarin da za a yi amfani da su domin narkar da gawar.

An yi kiyasin cewa kusan mutum 150,000 ne ke mutuwa a kowacce rana a duniya, kuma adadin na karuwa ne kamar yadda adadin mutanen duniya ke karuwa.

A wasu kasashe, ana karancin filin makabartu. Alal misali a Burtaniya an yi kiyasin cewa rabin makabartun kasar za su cika nan da shekaru 20 masu zuwa.

A wasu sassa a birini Landan, hukumomi sun daina shirya bukukuwan jana'iza, kuma birnin ya fara amfani da tsofaffin kaburbura, ta yadda ake kara nitsar da tsohuwar gawa cikin kasa, a kuma sanya sabuwa a kai.

Masu rajin kafa wannan sabuwar fasahar, sun ce Amurka tana amfani da akwatin gawa da nauyinsa ya kai Tan miliyan 1.1, da kuma karfen da ya kai Tan 14,000 a kowace shekara.

Ga masu kona gawa, an yi kiyasin cewa kona gawa daya kacal na haifar da iska mai guba da yawanta ya kai Kilogram 320.

Don haka sun ce idan ba a dauki matakai ba, guba mai hatsari za ta yi ta yaduwa tsakanin al'umma, wanda kuma zai haifar da yawan gurbacewar muhalli.

Labarai masu alaka