Ko Buhari ya gaza wajen farfaɗo da harkar ilimi a Nigeria?

Dr Aliyu Tilde manazarci ne kan bangarori daban-daban a Najeriya
Image caption Dokta Aliyu Tilde manazarci ne kan bangarori daban-daban a Najeriya

Dokta Aliyu Tilde wani manazarci a Najeriya, ya yi duba kan ayyukan gwamnatin tarayyar Najeriya kan ilimi a shekaru biyu da ta gabata, karkashin mulkin Buhari. Shin akwai abin da ya sauya?

An jima ana kokawa kan taɓarɓarewar harkar ilimin zamani a Najeriya. Wannan ɓangare ne da ke bukatar gyara a fannoni da yawa. Misali, dukkan azuzuwa daga firamare har zuwa jami'o'i a cushe suke da ɗalibai.

A makarantun firamare a kan samu sama da yara 50 cikin aji daya, lokacin da a jami'o'i ta kan kama har sama da dalibai 500 ke ɗaukar darasi wajen malami guda cikin ɗakin karatu da ya cika ya batse har waje.

Akwai ƙarantar ƙwararrun malamai a kowane mataki na ilimi, da rashin kayan aiki a azuzuwa da ɗakunan bincike, kamar yadda ake da ƙarancin sabbin litattafai da mujallolin ilimi a ɗakunan karatu. Ga kuma satar jarrabawa da ya zama ruwan dare a kowane mataki.

A ƙarshe, akwai ƙarancin kuɗaɗen kashewa kan ilimi a kasafin kuɗin ƙasar inda hatta Gwamnatin Tarayya sau da yawa ke kashe kasa da kashi 6 cikin 100 na kasafin kuɗinta a kan ilimi. Wannan shi ya sa jami'ar Najeriya guda ɗaya tak ce ta samu shiga cikin jerin jami'o'i dubu mafi inganci a duniya.

Don haka gyara a sha'anin ilimi na daga cikin abin da 'yan Najeriya musamman iyaye da ɗalibai da malaman makarantun zamani suka sa rai sabuwar gwamnatin APC za ta duƙufa a kansa da zarar ta hau kan mulki a 2015.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya yi wa 'yan Najeriya alkawura da dama lokacin yakin neman zabensa

Ita ma jam'iyyar APC ɗin, ta ɗau wannan ƙudirin inda ta yi wa masu zaɓe alƙawurra a ƙalla 30 a kan gyaran ilimi, adadi mafi yawa da ta yi a fanni guda cikin alƙawurra fiye da 200 da ta yi a lokacin.

Yau shekara biyu ke nan da jam'iyyar APC din ta hau kan mulki a Najeriya. 'Yan ƙasa za su so su san: Shin, wanne sauyi aka fara samu a fannin ilimi kuma alƙawura nawa jam'iyyar ta cika cikin tarin wadanda ta ɗauka lokacin kamfen ɗinta?

Ga dukkan alamu, abin da kamar wuya. Don har yanzu rahotanni na nuna cewa matsalolin da suka addabi sashin ilimin, wanda muka zayyana kaɗan daga cikinsu a baya suna nan daram, ba wanda ya gusa.

Ba abin da zai nuna wannan fiye da cewa ba a samu wani gagarumin sauyi ba a kason da ake bai wa ilimi a kasafin kuɗin ƙasar a matakin tarayya da jihohi bai daya.

A kasafin shekarar 2016, kashi 6.1 cikin 100 ne kawai Gwamnatin Tarayya ta ware wa sashin ilimi. In aka haɗa da wanda jihohi suka ware, ƙasar ta ware wa ilimi kashi 8% ne na kuɗaɗen kashewar gwamnatocinta. A hakan ma, kashe 43.7 cikin 100 zai je ne wajen biyan malamai.

Wasu ƙungiyoyi uku masu rajin kare dimokraɗiyya da ke bibiyar alƙawurran da jam'iyyar APC ta wa 'yan Najeriya sun kasa faɗin ci gaban da aka samu a kan alƙawurra guda 30 ɗin da jam'iyyar ta yi.

Ci gaban da aka samu

Amma duk da haka akwai abubuwa na gyara da za a ce gwamnatin ta yi. Waɗannan sun haɗa da soke jami'o'in ilimin tarbiyya - wato Universities of Education - da tsohuwar gwamnati ka kafa; da ƙoƙarin daidaita kalandar karatu ta jami'o'i; da shawo kan malaman kar su je yajin aiki; da soke jarrabawar kafi-JAMB (Post UME) da jami'o'i ke yi lokacin ɗaukar dalibai ; da soke darasin addini - wato IRK da CRK - a tsarin koyawarwan ƙasar, wanda aka maye shi da ilimin ɗa'a; da daidaita kuɗaɗen da iyaye za su biya wa 'ya'yansu a Kwalejojin Gamayya na ƙasar.

Haka kuma ƙasar ta sa hannu a yarjeniyoyin ilimi da ƙasashe kamar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Pakistan da Falasɗinu da Koriya ta Kudu da Rasha da kuma Aljeriya.

A ƙarƙashin waɗannan yarjeniyoyi, ana sa ran fannin ilimi a ƙasar zai amfana da samun taimako ta fannin kimiyya da fasaha da samun guraben karatu kamar ɗalibai 78 da aka tura ƙasashen Rasha da Aljeriya bara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu sharhi na ganin da sauran rina a kaba wajen inganta harkar ilimi a Najeriya

Ci-baya

A wani ɓangaren kuma, za a iya cewa an samu ci baya a fannin ilimi a ƙarƙashin wannan gwamnatin. Alal misali, soke amfani da katin kuɗin Mastercard ya jawo wahalhalu da yawa ga ɗaliban Najeriya da ke ƙasashen waje, inda suke kasa amfani da kuɗaɗensu don cin abinci da biya wa kansu wasu bukatun yau da kullum.

Wannan ya jefa da yawa daga cikinsu cikin halin ha'ula'i. Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan alawus-alawus na ɗaliban da ta tura karatu a ƙasashen waje har ta kai ga wasu sun daina karatun, wasu kuwa sai da suka koma dogaro da danginsu don samun abin da za su kashe.

Ɗaliban da jihohi suka tura karatu a ƙasashen waje suma haka suke ta fama da waɗannan wahalhalun da rashin Dala da za su biya kuɗin makaranta da lura da kawunansu.

A baya-bayan nan, gwamnati ta ce ta bai wa bankuna kuɗaɗen ƙasashen waje don biyan kuɗaɗen makaranta , amma an ci gaba da kokawa kan yadda bankunan ke ɓoye kuɗaɗen su ƙi bai wa mabukata.

Haka ma ɗalibai da malamai da 'yan kasar baki ɗaya ba za su iya amfani da katunan bankinsu ba don sayen litattafai daga dillalan litattafai da mujallu irinsu Amazon. Duk da kokawa da ake yi, Babban Bankin Najeriya ya jaddada dokar hana amfani da katin banki a kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Da sauran rina a kaba

Da alama za a ɗau lokaci mai tsawo kafin harkar ilimi ta gyaru a Najeriya.

A bara kaɗai, akwai sama da ɗalibai miliyan guda da rabi da suka nemi shiga jami'a a ƙasar; ɗaliban firamare kaɗai sun kai miliyan 25; makarantun firamare na gwamnati kuwa sun kai 54,434 da malamai 631,160.

Kawo sauyi a fanni mai faɗi irin wannan ba zai yiwu ba sai da kashe kuɗaɗe masu yawa, da fito da tsari na zamani da zai warware matsoli da yawa na koyarwa, da rashin kwarewar malamai, da sauransu.

Don haka Hukumar UNESCO ta ba da shawara ga ƙasashe masu tasowa su ware abin da ya kai kashi 26 cikin 100 na kasafin kuɗinsu don raya ilimi muddin suna so su samu ci gaba mai ma'ana. To amma ina Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin APC ta tsaya a cimma wannan buƙata?

In aka duba kason ilimi a kasafin kuɗin 2017, sai a ce ma an samu ci baya don kashi 5.5 cikin 100 ne kawai ta ware wa ilimi. Wannan ya kasa kan na bara inda ta ware kashi 6.1 cikin 100.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Alƙalumma kuma sun nuna cewa wannan gwamnatin ba ta kai gwamnatin da ta wuce ware kuɗi wa harkar ilimi ba. Ko kasafin da ta yi wa ilimi na bara da bana sun kasa kason biliyan 426.5 da waccar gwanatin ta ware wa ilimi a shekarar 2013; da biliyan 493 a 2014; da biliyan 492 a 2015.

Wannan shi ya sa malaman jami'a irin su Dokta Laja Odukoya, Shugaban Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa reshen Jami'ar Lagos, suke ganin da sakel a yadda wannan gwamnati take gazawa wajen bai wa sashin ilimi isassun kuɗaɗe. A faɗar Dokta Odukoya, "akwai rikici a gaba."

Labarai masu alaka