Majalisa ta amince da dokar man fetur ta Nigeria

Kudurin dokar zai kawo sauyi mai amfani a bangaren man fetur na Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kudurin dokar zai kawo sauyi mai amfani a bangaren man fetur na Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudurin dokar yin sauye-sauye ga dokokin sarrafa mai da iskar gas a kasar wanda ake kira Petroleum Industry Bill.

Kwamitin hadin gwiwa da majalisar ta kafa kan man fetur da albarkatun gas ne ya gabatar da rahoton a ranar Alhamis.

Bayan duba ga kudirin, tare da yin 'yan kananan sauye-sauye, majalisar ta amince da kudurin, inda ya kusa zama doka.

An shafe shekaru ba a amince da kudurin ba saboda hakan ba zai rasa nasaba da fatan da ake da shi na kawo sauye-sauye a bangaren man fetur da iskar gas na Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki ya ce, " Ina yi wa Majalisar Dattawa murna na amincewa da suka yi da wannan kuduri wanda ya dade a majalisar

Sharhi, Naziru Mika'il

Kuduri ne da yake son kawo sauye-sauye kan yadda ake gudanar da al'amura a bangaren man fetur, da kuma kawo sauye-sauye a kamfanin mai na kasa NNPC, ta yadda kamfanin zai dinga gogayya da manyan kamfanonin mai na duniya domin samun riba maimakon faduwar da yake yi wanda ake ganin zargin cin hanci da rashawa da ya adabi kasar ne ya jawo hakan.

Akwai zargin cewa wasu manyan kamfanonin mai na duniya kamar ba sa farin ciki da kudurin, shi ya sa ake ganin kamar hake ne ya jawo tarnaki a baya.

Ainihin kudurin ya zo ne daga bangaren zartarwa, amma amincewar na yanzu ya zo ne daga bangaren 'yan majalisa wato yunkurinsu ne na ganin an kawo sauyi a wannan fanni shi yasa aka zo wannan gaba.

Sai dai har yanzu da sauran tafiya domin akwai bukatar Majalisar Wakilai ita ma ta amince da wannan kuduri sanan kuma a aika shi zuwa fadar shugaban kasa kafin daga bisani ya zama doka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin cin hanci ya mamaye bangaren man fetur na Najeriya

Labarai masu alaka