Wani zai sha ɗaurin shekara 6 kan kalaman da ya yi a Facebook

Yonatan Tesfaye zai sha daurin shekara shida Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Yonatan Tesfaye zai sha daurin shekara shida

Wani ɗan jam'iyyar adawa a kasar Habasha Yonatan Tesfaye, zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekara shida bayan da aka kama shi da laifin goyon bayan ta'addanci a kalaman da ya yi a Facebook.

Wata jaridar kasar Addis Standard, ta ruwaito labarin inda ta kara da cewa kotun ta yi masa hanzari inda ta saurari wasu hujjojinsa, ta kuma yi masa sassauci wajen yanke hukuncin.

A farkon wannan watan ne, kungiyar Amnesty International ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ba a yi wa mutumin adalci ba.

An kama shi ne a watan Disambar 2015 a lokacin da zanga-zangar adawa da gwamnati da ake yi a yankin Oromia ke kara yaduwa.

Hukumomi sun nuna rashin amincewa da rubuce-rubuce masu yawa da ya yi da suka hada da inda ya ce, "gwamnati na amfani da karfin tsiya a kan mutane maimakon tattaunawar zaman lafiya."

An yi ta Allah wa-dai da Habasha kan amfani da dokokin da ake adawa da ta'addanci don rufe bakin 'yan adawa.

Labarai masu alaka