Takaddama ta kaure a Niger kan sarauta

A Jamhuriyar Nijar, wata takaddama ta kaure tsakanin wasu bangarori 2 da ke neman sarautar garin Tsibiri da ke cikin yankin Dogon Dutsi a jahar Doso.

Hakan ya biyo bayan wani hukunci da wata babbar kotu a Yamai ta yanke ranar Alhamis inda ta hana bangaren Arawa yin takaran neman Sarautar.

Sai dai wani mai magana da yawun bangaren Arawa, Shekarau Kwabo Sarkin Nassarawa ya ce ba zasu amince da matakin ba, sai dai a yi musu ta su masarautar.

Ya kuma yi zargin cewa an sanya siyasa kan batun masarautar.

Ana su bangaren Alhaji Salisu mai Fada, daya daga cikin masu neman sarauta a bangaren Gubawa ya ce tun da kotu ta yanke shari'a bai kamata bangaren Arawa su rika ja da hukuncin kotu ba.

An dai sha fuskanta takaddama akan sarauta a Jamhuriyar Nijar, lamarin da kan kaiga mummunar rikici har da asarar rayuka.