Fursunoni sun tsere a gidan yari a Brazil

Yan sandan Brazil sun cafke 9 daga cikin fursunoni 91 da suke tsere Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yan sandan Brazil sun cafke 9 daga cikin fursunoni 91 da suke tsere

Kimanin fursunoni casa'in da daya ne suka tsere daga wani gidan yari a arewa maso gabashin Brazil bayan da suka sulale ta wata 'yar karamar hanya dake karkashin kasa.

Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda a yankin Parnamirim, dake jihar Rio Grande do Norte, sun cafke mutum tara daga cikin fursunonin yayin da suke fafutikar nemo sauran da suka tsere.

Wannan lamari dai ya faru ne 'yan watanni bayan da wasu fursunoni 56 suka tsere daga wani gidan yari a jihar sakamakon kazamin fada tsakanin wasu gungu da basa ga maciji da juna.

Kamar dai akasarin gidajen yari da dama a Brazil, gidan yarin na Parnamirim ya yi matukar lalacewa baya ga cunkuson fursunoni da ake fuskanta.