Shugabannin kasashen G7 zasu fara taro a Italiya

Donald Trump ya isa birnin Sicily da matar sa ranar alhamis don halartar taron G7 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Donald Trump ya isa birnin Sicily da matar sa ranar alhamis don halartar taron G7

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki wato G7 za su fara wani taro a birnin Sicily na kasar Italiya,

Taron dai shi ne na farko da shugaban Amurka Donald Trump zai halarta yayin da yake kammala ziyarar sa a wasu kasashen duniya.

Tun bayan harin da aka kai a birnin Manchester, ana saran shugabannin za su amince da bukatar kara matsa kaimi don yaki da ta'addanci a duniya.

Sai dai wakilin BBC kan harkokin dilomasiyya ya ce Mr Trump zai fuskanci adawa kan wasu manufofi da suka hada da matsayin sa game da sauyin yanayi.