Manchester: Wayar salula ta ceci ran wata a harin bam

Lisa Bridgett Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Lisa Bridgett na asibiti tare da iyalanta

An nuna hotunan wata wayar salula wacce ake zaton ta taimaka wajen ceto rayuwar wata mata 'yar yankin Gwynedd, kuma matar da ta sami raunuka masu yawa a lokacin da aka kai harin bom a birnin Manchester.

Matar mai suna Lisa Bridgett 'yar asalin garin Pwllheli na kasar Wales ce, tana cikin amfani da wayar ne a ranar Litinin, lokacin da bam din ya tashi, kuma wani notin karfe ya buge ta.

Lamarin ya sa ta rasa yatsarta ta tsakiya kuma notin ya fasa wayarta da kuncinta, inda ya makale a cikin hancinta.

Mijinta ya ce yana ganin wayar ce ta karkatar da notin ta kuma rage karfinsa.

Hakkin mallakar hoto Steve Bridgett / Facebook
Image caption Ana ganin wayar salular Lisa Bridgett ta ceci rayuwarta

Harin da aka kai a dandalin wasanni na Manchester Arena ya kashe mutum 22 kuma ya raunata wasu 64. An kama mutane takwas a sanadiyyar harin da Salman Abedi ya kai.

Madam Bridgett waddad ta tafi wajen kallon mawakiyar tare da 'yarta da kuma 'yar kawarta, ta ce ta yi "sa'a ba ta halaka ba", in ji mijinta Steve.

An yi mata tiyata ranar Talata kuma za a sake yin wani tiyatar ranar Alhamis bayan da aka gano ta sami raunuka a wurare daban-daban har da karaya a kafarta da wani katon rauni a cinyarta.

Mista Bridgett ya shiga shafinsa na Facebook yana cewa, "Ina ganin amfani da wayar salularta a daidai lokacin ya ceci rayuwata."

"Da alama wayar ta karkatar da notin kuma ta rage masa sauri kwarai", in ji shi.

Mista Bridgett ya ce shi da mai dakinsa suna mika godiyarsu ga jami'an 'yan sanda da ma'aikatan asibiti, da wani mutum mai suna Peter, "domin taimaka wa Lisa da suka yi daga wurin harin zuwa asibiti".

Labarai masu alaka