Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a wannan makon

Wasu zaɓaɓɓun hotuna abubuwan da suka faru a sassan Afirka a makon nan.

Relatives of the rescued Chibok girls greet each other as they wait to be reunited with their children in Abuja, Nigeria May 20, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Asabar ne, 'yan uwan 'yan matan Chibok 82 da aka sako a watan Mayun nan, suke shewa da tafi tare da gaisawa da juna a lokacin da suke jira domin ganawa da 'ya'yan nasu.
A father being reunited with one of the released Chibok girls in Abuja. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ranar farin-ciki ce ta musamman ga 'yan uwa da suka dade ba su gana ba, wadanda suka yi tafiya mai nisa daga jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya zuwa babban birnin kasar, Abuja.
Families unite with the released Chibok girls Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan matan da aka sako na cikin 276 da mayakan Boko-Haram suka yi garkuwa da su daga makarantar 'yan mata ta Chibok a shekarar 2014
People hold placards picturing Ethiopian Candidate for the post of Director General of World Health Organization (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, during a rally on his support, in front of the United Nations offices. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata ne, 'yan kasar Habasha suka taru a kofar hedikwatar Hukumar Lafiya ta Duniya a Geneva da ke Switzerland, don nuna goyon bayansu ga sabon shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, kuma shi ne dan Afirka na farko da ya fara shugabantar Hukumar.
Supporters of Dakar mayor Khalifa Sall carry placards and chant slogans during a demonstration calling for his freedom from detention Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya bayan magajin garin Dakar ta kasar Senagal Khalifa Sall, sun yi gangami a birnin, suna kira da a sake shi, wanda aka kama bisa zargin zamba da kuma halatta kudaden haram.
An Egyptian seller dusts a traditional Ramadan lantern called "fanous" at his shop stall ahead of the Muslim holy month of Ramadan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dauki wannan hoton ne a ranar Laraba lokacin da wani dan kasar Masar yake karkade fitilar da yake sayarwa wacce ake amfani da ita a watan azumin Ramadan, a birnin Alkahira.
Egyptian women carry traditional Ramadan lanterns called "fanous" ahead of the holy fasting month of Ramadan in Cairo, Egypt May 24, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana amfani da irin wannan fitilar da ake kira 'fanous' wajen yin ado lokacin watan azumin Ramadan.
A woman buys a packet of maize flour subsidised by the government at a supermarket in Kenya's capital, Nairobi, on Wednesday. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Laraba ne wata mata take sayen jakar garin masara a wani shagon sayar da kayayyaki wadanda gwamnati take tallafawa wajen rage farashinsu.
A woman buys oranges from a street vendor in central Harare, Zimbabwe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A nan kuwa wata mata ce ke sayen kayan marmari a gefen titi a Harare, babban birnin Zimbabwe.
A robot performs during the final of the national robotics competition on May 20, 2017 at the Marius Ndaye stadium in the Senegalese capital Dakar. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar ne, aka yi gasar mutum-mutumi ta kasa, ta karshe a Dakar babban birnin Senegal.
A robot performs during the final of the national robotics competition at the Marius Ndaye stadium in the Senegalese capital Dakar. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Senegal ce ta shirya gasar, don janyo hankalin matasa da kara musu sha'awar ilimin kimiyya.
A competitor prepares a robot during the final of the national robotics competition Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dalibai da dama sun shiga gasar, wadda aka yi a filin wasa na Marius Ndiaye, inda ake wasan kwallon raga.
A robot performs during the final of the national robotics competition on May 20, 2017 at the Marius Ndaye stadium in the Senegalese capital Dakar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutum-mutumin na da na'urori da danja masu daukar hankalin jama'a.
Residents of drought-hit Cape Town in South Africa crowd at night around a fresh water source from a stream off Table Mountain to collect safe drinking water amidst the water crisis Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mazauna Cape Town da suke fama da fari a kasar Afirka Ta Kudu sun taru a kan wani ruwa mai kyau da aka debo daga koramar 'Table Mountain' da daddare, don su samu su karbi wanda za su sha.
On Friday, French President Emmanuel Macron and his Mali counterpart President Ibrahim Boubacar Keita inspect a guard of honour during a visit in Gao, northern Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Juma'a ne, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Mali Ibrahim Boubacar Keita ke karbar gaisuwar girmamawa a birnin Gao, da ke arewacin Mali, a ziyarar da shugaban Faransan ya kai Mali.

Images courtesy of AFP, EPA, Getty Images and Reuters

Labarai masu alaka